Karya Dan majalisa Zulyadaini Karaye Yake yi wa Mai Martaba, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Ya ku Jama’ah, lallai ku sani, wallahi abun mamaki kuma abun ban dariya baya karewa a kasar nan tamu Najeriya. Wato duk wani shedanin dan siyasa, wanda ya kasa yiwa jama’ar sa komai, mara kunya, da ya bushi iskar sa babu wadanda ya raina sai masu Martaba, iyayen mu kuma Sarakunan mu na Musulunci! Duk wani wanda ya kwaso tarkacen sa da yaye-yayen sa da shirmen sa ba yada wurin zube wa sai akan wadannan bayin Allah, wadanda ba dare ba rana suna ta fadi-tashin ganin yaya za’a yi a samu zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a cikin al’ummah!

Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Abun dariya, wai yaro ya tsinci hakori, yau kuma kwatsam, sai muka wayi gari da wani shirme daga wani wawan dan majalisa daga jihar Kano. Wannan mutum, wai bai ga wanda zai yiwa karya, kage da sharri ba sai Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, kawai ba don komai ba sai domin ya samu shiga wurin mai gidan sa, ko kuma don ya cimma wani burin sa na samun abun duniya.

Idan baku manta ba, kwanakin baya Mai Martaba Sarki yayi kokarin kawo gyara game da kura-kurai da ake tabkawa a cikin sha’anin aure da kuma zamantakewar aure, domin nemar wa mata ‘yancin su da hakkin su akan zaluncin da ake yi masu da sunan aure. Aiki ne da har yanzu ana nan ana yi. Wannan yunkuri da Mai Martaba Sarki yayi abu ne mai kyau. Domin aiki ne da ni a sani na aka dora wa malamai, masana, masu mutunci da nagarta, masu amana a cikin al’ummah. Ba aiki ne da za’ayi a cikin jahilci ba ko son zuciya. Sannan a lokacin Mai Martaba Sarki yayi wani bayani, wanda jahilai da masu bin son zuciya ba su fahimci me yake nufi ba. A Musulunci, mun san cewa marin mutum haramun ne. Ko dan ka da ka haifa, ko matar ka, ka mare su baya halatta. Domin fuskar dan Adam tana da daraja, shi yasa Manzon Allah (SAW) ya hana a taba fuska wurin hukunta wani. Sanin haka da wasu dalilai, yasa Mai Martaba yace shi kam idan mijin ‘yar sa ya mare ta, yana iya cewa ta rama. Dukkanin mu mun san meye Mai Martaba Sarki yake nufi, mun fahimci zancen sa. Sarki sam ba yana zuga mata ba ne suyi fada ko hayaniya ko hargitsi ko tashin hankali da mazajen su. Kawai ‘yancin mata ake kokarin karewa, sanadiyyar cin zalun din su da maza suke yi da sunan aure. A yau sai ka ga mutum yayi wa matar sa dukan kawo wuka, ya karya ta, ya ji mata mummunan rauni, ya kore ta ko ya bar ta cikin damuwa da ‘ya ‘ya ko cikin yunwa. Duk wannan ne fa ake son a kawo karshen sa a cikin al’ummah da izinin Allah. Amma wai sai aka wayi gari a yau, wannan dan majalisa, da yake bai gane me ake nufi ba, ya fito kafafen yada labarai na zamani da radio, wai yana cewa, Mai Martaba Sarki ne yake tunzura mata suna kashe mazajen su. Saboda kawai an samu wasu mata marasa tarbiyyah suna cutar da mazajen su, shine wannan jahilin dan siyasa yake danganta wannan masifa ga Mai Martaba Sarkin Kano!

Ga karyar tasa na hakaito maku kamar yadda ya fada, ya kuma yada ta. Shi yasa muka ga ya zama wajibi mu kuma mu bayyanawa al’ummah cewa wannan dan majalisa wallahi karya yake yi, kuma abun da ya fada ba gaskiya bane. Ga abunda yake cewa:

“Sarkin Kano Ne Ya Tunzura matan arewa suke kashe mazajen su – Hon. Zulyadaini Hon. Zulyadaini Sidi Mustapha Karaye, ya bayyana cewa Sarkin Kano ne ya tunzura matan arewa suke kashe mazajen su. Idan ba’a manta ba akwai wani lokaci da Sarkin ya bayyana cewa duk macen da mijinta ya mare ta ta rama. Wannan Sarki yana daya daga cikin masu ra’ayin ganin an daidaita tsakanin maza da mata, a lokacin da yayi wannan maganar duk kafafen yada labarai na kasar nan sai da suka yada labarin. A matsayinsa na Sarki uban al’ummah bai kamata ya fadi haka ba, domin kuwa kofar gabatar da barna ya bude, wanda a yanzu haka ake ganin sakamakon abin. Iyaye mata tunaninsu ba iri daya bane dana maza, suna da matukar rauni ta bangaren da ya shafi tunani, idan ran mace ya baci babu abinda ba zata yi ba, yayin da shi kuma namiji a wannan lokacin zai iya danne zuciyarshi. Kuskure ne babba a nuna wa mata cewa daya suke da maza, har kuma a basu fatawar cewa duk wacce mijinta ya mareta ta rama. Saboda haka muna kira ga duk wasu masu ra’ayi na boko aqeedah, da su gane girman hatsarin da suke kokarin jefa mutane ciki, kullum tunaninsu shine su canja hukuncin da Allah ya gindaya, Allah ne ya hallice mu, yafi mu sanin dalilin da ya sanya ya shar’anta.”

Ya ku ‘yan uwa, wannan shine jawabin da wannan dan majalisa yayi, kuma ake ta yada wa. Yanzu don girman Allah a ina ne Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya taba kira a daidaita mace da namiji? Kuma a ina ne Mai Martaba Sarki ya taba zuga mata su kashe mazajen su? Shin shi wannan wawan dan majalisar, jahili, kidahumi, ya dauka cewa Mai Martaba Sarki irin sa ne wanda bai fahimci Addini ba? Mutumin da duniya ta shaida ilimin sa, kana nufin zai fadi magana a cikin jahilci ne? Me yasa shin wai mutane basa jin tsoron Allah ne? Me yasa mutane basu yiwa mutane adalci ne? Kana nufin akwai wani jahili irin ka da zai yarda cewa wai Mai Martaba Sarki yana zuga matan arewa su kashe mazajen su? Haba jama’ah! Ai idan mai fada wawa ne, to masu sauraro ba wawaye bane!

Daga karshe ina rokon Allah ya shiryi ‘yan siyasar mu su fahimci Martaba da darajar wadannan Sarakuna namu bayin Allah. Allah yasa su gane cewa wadannan Sarakuna shugabanni ne na addini. Kuma su fahimci cewa suna wakiltar addinin mu ne da al’adun mu, amin.

Kuma dan majalisa Zulyadaini Sidi Mustapha Karaye, idan ma har yana hassada ne da matsayin Mai Martaba Sarki ne, to ya sani Sarki yin Allah ne, ba shine ya dora kan sa ba, Allah ne yayi ikon sa har ya zama Sarkin Kano kuma jagoran Kanawa baki daya. Kuma da yardar Allah Mai Martaba Sarki, gani-nan-bari-nan, domin al’amarin daga Allah ne!

Kuma dan majalisa Zulyadaini da ire-iren sa ya kamata su sani, Masarauta daya ce a jihar Kano. Kuma har gobe ita kadai ce al’ummar jihar Kano na gaskiya ba bakin haure ba suka sani kuma suke yiwa biyayya tsakanin su da Allah. Ita ce kadai masarautar da take da tutar Musulunci, Tagwayen Masu, Malafar Dabo, Wukar Yanka da Sandar Girma na Sarki mai daraja ta daya tun Fil azal. Ka sani, kai da duk wani hasidin iza hasada, Masarautar Kano Masarauta ce ta din-din-din, mai mutunci, mai daraja, kuma wadda ta ke da asali a tarihin kafuwar Musulunci a kasar Kano.

Amma Masarautun bogi, suna nan a matsayin su na bogi har abada, kuma haka suke a zukatan al’ummah. Ba su da kima da daraja, saboda an kirkire su ne ba don komai ba sai domin raba kawunan Al’ummar jihar kano. Wanda kuwa kowa ya sani, rarraba kawunan Al’ummah ba halin mutanen kwarai bane, hali ne na mutane marasa daraja, wadanda suke satar dukiyar al’ummah, da kuma yaki da gaskiya da masu fadin gaskiya. Mutane ne da suka siffantu da rashin gaskiya da ha’inci da almubazzaranci da dukiyar al’ummar da suke shugabanta. Ina rokon Allah ya shirye su kuma ya ganar da su gaskiya ya basu ikon bin ta, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwanku Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a samu Imam a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761

Share.

game da Author