Fitaccen kakakin gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwa wanda yayi suna wajen kare muradin gwamna El-Rufai da tallata ayyukan jihar ya samu shiga cikin jerin sabbin Kwamishinonin gwamna Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya aika da sunayen wadanda za su zama kwamishinoni a gwamnatinsa a wannan zango ta biyu.
El-Rufai ya aika da sunayen mutane 11 saura mutane uku da ya ce zai aika daga baya.
Ga Jerin sunayen:
1. Ja’afaru Ibrahim Sani Ma’aikatar Kananan hukumomi
2. Idris Samaila Nyam Ma’aikatar Kasuwanci
3. Shehu Usman Makarfi Ma’aikatar Ilimi
4. Ibrahim Garba Hussaini Ma’aikatar kasa
5. Kabir Muhammad Mato Ma’aikatar Matasa da Wasanni
6. Balaraba Aliyu-Inuwa Ma’aikatar Ayyuka
7. Samuel Peter Aruwan Ma’aikatan Tsaron Cikin Gida
8. Fausat Adebola Ibikunle Ma’aikatar tsare-tsaren Birane
9. Mohammed Bashir Saidu Ma’aikatar Kudi
10. Hafsat Mohammed Baba Ma’aikatar jindadi da ci gaban Al’umma
11. Aisha Dikko Ma’aikatar Shari’a