Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi ƴan Najeriya da su riƙa tauna magana kafin su furta musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalan tsaro a kasar nan.
Buhari ya bayyana haka ne a takarda da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ranar Litini.
Shugaba Buhari ya ce bai dace ace wai waɗanda suke kan madafan iko sannan shugabannin al’umman suna yaɓo zantuka ratatata ba tare da suna tauna aɓin da zasu furta ba.
” Dole ne fa shugabannin su zo a haɗa kai ne wajen ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro da muke fama da shi a kasar nan ba ariƙa magana da son rai ba.
” Ba ya ga haka ƙiriƙiri gashi an maida maganar tsaro a ƙasarnan siyasa. Shima yin haka ba abune da ya dace ace ana yi ba. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana da mahaifin ita marigayiya da mahara suka kashe Rueben Fasoranti.
” Hakanan shima mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, ya kai ziyara har gidan mahaifin marigayiya Olakunrin.Amma yadda wasu suka maida abin siyasa sam babu alfanu a ciki da kuma yin haka.
A karshe Buhari ya yi kira da a haɗa hannu tare a kauda matsalar tsaro a ƙasar nan.
Idan ba a manta ba, ƴan fashi da makami sun kashe ƴar shugaban kungiyar Afenifere, Rueben Fasoranti a hanyar Akure ranar Juma’ar da ya gabata.
Hakan ya jawo cece-kuce inda wasu da dama a wannan yankin da ya hada da ƙungiyar Oodua ke cewa wai Fulani mahara ne suka kashe Olakunri.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Buhari wasika ta musamman yana kira ga gwamnatin Buhari ta maida hankali matuka wajen shawo matsalar tsaro da ake fama da shi a Najeriya.