Gwamnatin jihar Zamfara karkashin gwamna Bello Matawalle ta nada kwamiti domin daukar matasa 3800 aiki.
Kamar yadda Darektan Yada Labaran gwamnan Matawalle, Yusuf Idris ya sanar ya ce za a dauki wadannan matasa a wani sabon shirin da gwamnatin jihar ta kkirkiro na koyar da matasa sana’o’i a jihar.
A wannan shiri da za ta yi, za a dauki matasa Goma-Goma daga kowacce mazaba dake jihar. A lissafe za a dauki matasa 3800 kenan.
Idris ya ce akwai mazabu 114 a kananan hukumomin jihar 14.
An nada Usman Dankalili a matsayin shugaban wannan shiri shi kuma Kabiru Mai-Palace sakataren wannan shiri.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Ibrahim Mahe, Basira Musa, Sa’idu Maishanu, Husaini Dan-isa, Oba Obama, Murtala Jangebe and Tukur Limantawa.