Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta fasa aikin gina rugage domin amfani Fulani makiyaya ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa ya yi tare da Shugaba Muhammadu Buhari Buhari a Fadar Shugaban Kasa.
Shirin gina rugage dai shiri ne da gwamnatin tarayya ta yi niyyar kafa wa Fulani makiyaya matsugunai domin daina karakainar zuwa kiwo wurare masu nisa.
Za a samar da ababen saukaka kuncin rayuwa kamar kananan madatsun ruwa, asibitoci da makarantu da kuma mayanka babbobi da kasuwanni. Har ma da asibitin dabbobi.
Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin bayan da ya kasa samun karbuwa a fadin kasar nan.
Gwamna David Umahi na Jihar Delta ne ya bayyana sanarwar dakatar da shirin bayan fitowar su taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar ranar Laraba tare da Shugaba Muhamadu Buhari.
Sai dai kuma shi gwamnan Gombe, ya bayyana cewa, “a maganar nan da ke yi da ku yanzu, Gwamnatin Jiar Gombe ta kebe fili mai eka 200,000 domin aiwatar da shirin kafa rugagen Fulani makiyaya a jihar.
“Don kawai wasu jihohi sun ki amincewa da shirin, hakan ba zai sa mu a jihar Gombe mu ki amincewa da shirin ba.
“Za su aiwatar da shirin, domin mu dai mu na ganin cewa zai zama alheri ga Fulani, wadanda a halin yanzu ke faman wahalalhalun yawon kiwon dabbobin su.”