Jakadan Birtaniya a Amurka ya yi murabus

0

Jakadan Birtaniya a kasar Amurka, Kim Darroch, ya yi murabus a yau Laraba, bayan fitar wasu munanan kalaman da suka jefi juna shi da shugaban Amurka Donald Trump.

Sabanin dai ya samo asali ne tun cikin makon jiya, inda aka fallasa wani bayanin sirri dangane da Trump, wanda jakadan Birtaniya ya aika wa kasar sa a asirce.

A cikin bayanin da Darroch ya aika wa kasar sa, ya bayyana Trump a matsayin wani shugaba wanda “notikan da ke daure da kan sa duk suka kwance.”

Ya bayyana Trump a matsayin wanda bai san abin da ya ke ba, kuma dan ragabza da hauragiya.

Jakadan na Birtaniya ya kara bayyana Trump cewa shugaba ne wanda a karshe zai kai kasar Amurka ya baro, sannan kuma zai fuskanci wulakanci a nan gaba, idan aka dawo daga rakiyar sa.

Ya nuna Trump a matsayin wani dan bankaura, jagaliya da kuma gargajigan da bai dace a ce ya na shugabanci ba, ballantana kuma shugabancin kasaitacciyar kasa kamar Amurka.

Wannan bayanai da aka fallasa sun harzuka Trump, wanda shi kuma a jiya Talata, ya shiga shafin sa na twitter ya rika surfa wa jakadan na Birtaniya zagi.

Trump ya kira Jakadan Birtaniya na kasar sa da kalamai masu muni, inda ya kira shi, “mutumin banza”, saboda ya tura wa Birtaniya bayanai a asirce, inda ya ragargaji gwamnatin ta Amurka a karkashin mulkin Trump.

“Wannan shashashan jakada da Birtaniya ta turo mana a Amurka, ba irin mutumin da za mu yi murna da zaman sa ba ne. Sakarai ne, mutumin banza.” Inji Tump a shafin sa na twitter.

A cikin bayanan sirrin da Darroch ya tura Birtaniya, shi ma ya bayyana Trump a matsayin wani mutumin da ba shi da zurfin tunani, kuma “dan damaga.”

Shi ma Trump ya bayyana a shafin sa na twitter cewa, an fada masa jakadan “wani tumbuleken wawa ne”. Sannan ya nuna cewa shi bai ma san shi ba, amma ya na so a samu wani ya shaida masa cewa “a yanzu fa Amurka ce ta fi kowace kasa a duniya karfin tattalin arziki da kuma karfin sojoji da makamai.”

Da Trump ya koma kan Firayi Ministar Birtaniya, Theresa May, sai cewa ya yi ai ya ba ta shawarar yadda za ta warware matsalar rikicin kokarin ballewa daga Kungiyar Tarayyar Turai (Brexit), “amma da ya ke ita ma shashasha ce, sai ta bi son ran ta, shi ya sa ta kasa warware matsalar. Shi ya sa ta ke cikin bala’i.”

Sai dai kuma Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Jeremy Hunt, ya bayyana kalaman da Trump ya rubuta a shafin sa na tweeter cewa, “rashin girmama jama’a da rashin mutunta diflomasiyya ne.”

Ya kara da cewa: “Ai kai ma jami’an diflomasiyyar Amurka da ke Birtaniya su na aika wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da bayanai a kan mu!” Shi ma haka ya maida wa Trump martani a shafin sa na tweeter.

Jaridar Daily Mail ta ranar Lahadi ce dai ta fallasa bayanan sirri wanda jakadan na Birtaniya ya soki Trump.

A yau Laraba kuma jakadan ya aika wa Karamin Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya takardar yin murabus, tare da cewa kasar Amurka ba kasa ce da zai iya ci gaba da aiki a karkashin mulkin gwamnatin Trump ba ce.

Ya ce ya na ganin akwai bukatar a nada wani ya maye gurbin sa.

Tuni dai ana bayyana sunan wanda zai maye gurbin sa, tare kuma da nuna goyon bayan sa da manyan jami’an gwamnatin na Birtaniya suka yi, a kan cacar-bakin da ya ke yi shi da Trump.

Share.

game da Author