Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya ta fantsama afujajan farautar wasu sojoji biyar da suka sungumi makudan kudaden wani ‘VIP’ suka gudu da su.
Wasu magenta a cikin Sojojin Najeriya sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa makudan kudaden na Manjo Janar Hakeem Otiki ne.
Hakeem Otiki shi ne Babban Kwamandan Rundunar Mayaka ta 8 da ke Sokoto, watau GOC.
PREMIUM TIMES ta nemi Hakeem a yau Lahadi kafin buga wannan labari, amma ba ta same shi ba.
Sai dai kuma har yau ba a kai ga gano inda Hakeem ya samu dadaden ba, kuma ba a kai ga sanin inda aka yi niyyar kai kudin a Abuja ba, kafin wadancan ’yan rakiya su tsere da kudin da majiya ta ce sun kai “bilyoyin nairori.”
PREMIUM TIMES ta gano cewa bayan da sojojin biyar suka yi rakiyar motar da ke dauke da kudin zuwa dan karamin filin saukar jiragen sojoji da ke Jaji a Kaduna, sai suka ki loda su cikin wani jirgin yaki na soja da aka ajiye ya na jira su idan sun isa, a loda masa kudin ya cira sama da su, zuwa Abuja.
An tabbatar da cewa a cikin wata mota kirar Toyota Hilux aka loda kudin, wadda shi ma Manjo Janar Hakeem Otiki ya shiga ciki, su kuma sojojin biyar suka dafe musu baya a cikin wata karamar motar yakin soja samfurin Buffalo, mai rundumemiyar bindigar nan tashi-gari-barde a jikin ta.
A haka suka yi wannan doguwar tafiya kimanin kilomita 400 daga Sokoto zuwa Kaduna. Sai dai ba a san dalilin da ya sa ba su wuce da kudin zuwa Abuja a mota ba, sai suka tsara loda kudin a jirgin sojoji daga Jaji, Kaduna zuwa Abuja din.
Majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa, yayin da suka isa Jaji da kudin, sai wadannan sojoji biyar, wadanda a cikin su akwai Kofur biyu da Las Kofur uku, suka kulla tuggun da za su gudu da kudin su raba kawai.
“Daga nan suka cire kakin sojan su, kuma suka zubar da bindigogin su a cikin motar da suka je Jaji da ita.” Haka wata babbar majiya a cikin sojoji wadda ta san komai ya faru a lamarin ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Ba a dai tabbatar da adadin ko naira nawa ne zunzurutun kudin ba, amma dai majiyar mu ta cikin sojoji ta tabbatar da cewa “kudin fa biliyoyin nairori ne.”
PREMIUM TIMES ta kasa samun jin ta bakin Kakakin Hedikwatar Sojoji ta Abuja da kuma Kakakin Runduna ta 8 ta Sokoto damin jin ta bakin su a safiyar yau Lahadi, kafin buga wannan labari.
JA YA FADO JA YA KWASHE
PREMIUM TIMES ta zakulo cewa wadannan sojoji biyar da aka dora wa aikin rakiyar kudi daga Sokoto zuwa Kaduna, daga cikin Cibiyar Zaratan Sojojin Kundumbala ta Jaji ne Hakeem ya dauke su, su na yi masa aiki a Sokoto.
Shi ma Hakeem din daga Jaji aka dauke shi aka nada shi Babban Kwamandan Sokoto a cikin Maris. Shi kuma sai ya tafi da su domin su rika yi masa aikace-aikace.
Majiya a cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa sojojin sun dade su na lura da duk irin sabarkalar da manyan ofisoshin su ke yi a duk lokacin da manyan ofisoshin suka tura su yi musu wata hidima.
“Bayan sun dade su na yi musu hidimar jigila da zirga-zirgar hada-hadar kudade, sai wadannan sojoji suka yanke shawarar su ma bari su kwashi rabon su, domin su yi wa kan su ‘gyadar-Dogo’ – sama ’ya’ya kasa ’ya’ya.”
Haka wani jami’i ya shaida wa PREMIUM TIMES.
“Sojojin sun ci amana. Amma kuma hakan ta faru ne saboda kananan hafsoshin sojojin su na ganin yadda ake hauma-hauma da makudan kudade a gaban idanun su, alhali su kuma su kuma an ki a rika kula da su ana yi musu ‘ihisani’.”
“Shi ya sa sojojin suka yanke shawarar ballewa daga aikin soja, domin su gudu su mori makudan kudaden da suka sace.”
Wadannan jami’an sojoji da suka bai wa PREMIUM TIMES cikakken bayanin abin da ya faru, sun nemi a sakaya sunayen su, domin Hukumar Tsaro na Sojojin Najeriya ba ta so wannan labarin bahallatsa ya shiga duniya.
OLUWANIYI, AMINU, HARUNA, JOSHUA DA ABUBAKAR: Sun Ci Bilis Ko Sun Ci Kubeji?
Wata majiya ta bayyana sunayen sojojin da suka arce da kudin, cewa akwai: Kofur Gabriel Oluwaniyi da Kofur Mohammed Aminu; Sai kuma Kwamanda Haruna, Las Kofur Oluji Joshua, Las Kofur Hayatudden Abubakar.
Tuni dai aka fara neman su afujajan domin a kama su a hukunta su, kuma a kwace kudaden daga hannun su.
Majiya ta ce an yi amfani da wata na’ura inda aka gano wurin da suka dan makale, kafin daga bisani su nausa gaba.
Sannan kuma hukumar soja ta fara kokarin kullewa da kwace asusun ajiyar su na banki a daidai lokacin da ake fagamniyar farautar su.