Jami’in hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) Joshua Obasanya ya yi kira ga mutane da su rika gaggauta yin allurar rigakafi da zaran dabba ya ciji mutum domin gujewa kamuwa da cutar hauka na dabobbi.
Obasanya ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ya ce yin allurar rigakafin na kare mutum daga kamuwa da cutar hauka na dabbobi da ake kira ‘Rabies’ wanda ke iya yin ajalin mutum.
“Tabas da zaran dabba ya ciji mutum asibiti za su wanke raunin da mutum ya ji amma rashin yin allurar rigakafin ne ke haddasa wannan cutar.
“A na iya kamuwa da wannan cutar daga jikin dabba idan ya ciji mutum,ko ya yakusheshi ko kuma yawun dabba ya tabi ciwo a jikin mutum.
“Dabobbin da ke dauke da wannan cutar sun hada da kare, mage, jemage, zomo, da sauran su.
“Alamun cutar sun hada da haushi kamar kare, kumfar baki, hauka da saura sun sannan wadannan alamun kan bayyana ne bayan cutar ya dade a jikin mutum kamar daga kwanaki 15 bayan dabbar ta ciji mutum.
HANYOYIN GUJE WA KAMUWA DA CUTAR.
1. Yin allurar rigakafin cutar.
2. A tabbatar an yi wa dabobbi kamar su kare, mage da zomo allurar rigakafin cutar.
3. Toshe kowace kafa da jemage zai shigo gida ko kuma bishiyar da suke yawan zama.
4. Hana dabobbi kamar su kare da mage yawan yawo.
5. A guji cin naman kare, zomo, magen da ba a girka naman su yadda ya kamata ba.