Kamar yadda aka sani a duk ranar 28 ga watan Yuni na kowace shekara rana ce da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta kebe domin wayar da kan mutane a duniya game da cutar Hepatitis.
Cutar Hepatitis cutar ce dake kama hantar mutum sannan cutar kan dade a jikin mutum ba tare da an gano shi ba sai dai fa idan ba an yi gwajin cutar ne ake ganewa.
Cutar ta kasu zuwa Hepatitis A,B,C,D da E sannan bincike ya nuna cewa Hepatitis C da B ne suka fi kisan mutane a duniya.
Alamun cutar sun hada da canja kalar fatar jikin mutum zuwa kalar ruwan kwai, farin kwayar ido, amai, yawan jin gajiya a jiki,ciwon ciki,yawan zuwa bahaya da sauran su.
A wani binciken da WHO ta gudanar ya nuna cewa akalla mutane miliyan 325 na dauke da Hepatitis C da B sannan a duk shekara miliyan 1.4 na mutuwa daga cikinsu a duniya.
Binciken ya kuma nuna cewa cutar na daya daga cikin cututtuka uku dake kisan mutane a duniya.
Wadannan cututtuka sun hada da Ƙanjamau da tarin fuka.
A dalilin haka WHO ta yi kira ga gwamnatocin duniya musamman na kasashen dake tadowa dasu hada hannu da kungiyoyin bada tallafi domin kawar da cutar.
Kungiyar ta ce za a bukaci aƙalla dala biliyan shida domin daƙile yaɗuwar cutar a kasashe 67 dake tasowa a duniya.
HEPATITIS A NAJERIYA
Binciken da WHO ta gudanar ya nuna cewa Hepatitis C da B na neman zama ruwan dare a Najeriya.
A yanzu haka babu wanda ke da masaniyar adadin yawan mutanen dake dauke da wadannan cututtuka a Najeriya.
Hakan na da nasaba ne da rashin sani, rashin yin gwaji,rashin yin tanajin magunguna da kayan gwaji da gwamnatin kasarnan ba ta yi da sauran su.
A dalilin haka WHO ta yi kira ga gwamnatin Najeriya kan daukan darasi a namijin kokarin da kasashen India, Masar da Pakistan suka yi wajen daƙiƙe yaduwar cutar a kasashen su.
Discussion about this post