HATTARA MATA: Yin fidan kara girman nono na haddasa cututtuka – Likitoci

0

Kara girman nono ta hanyar yin fida tsohuwar yayi ne da matan kasashen waje suka dade suna yi.

Duk da cewa yin fidar na da matukar tsada hakan bai hana mata yin shi ba.

Kungiyar likitocin da suka kware a gyaran fatar mutum na kasar Amurka sun bayyana cewa kashi 40 bisa 100 na mata a Amurka na kara girman nonon su a 2000 a sakamakon bincike da sukayi.

A shekarar 2017 likitocin sun yi wa mata sama 400,000 fida domin karin girman nonon su.

Mata musamman masu kudi da fitattun ‘yan wasa sun fi yin wannan fida.

Matsalolin da kan fadwa macen da ta kara nonon ta.

1. Rashin iya shayar da da nono

2. Kamuwa da cutar dajin dake kama nono da jini da ake kira ‘Anaplastin Large Cell Lymphoma (ALCL0.

3. Nonon da aka kara wa mace girma kan fashe.

4. Yana hana samun isasshhen barci.

5. Haddasa ciwon kirji da ciwon baya.

6. Yawan gajiya

7. Rashin tsawon gashi a kai.

Share.

game da Author