HARKALLAR MAKAMAI: Ana neman cikon harsasai 780 a hannun Amosun-‘Yan Sanda

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta bayyana cewa har yanzu tsohon gwamnan Jihar Oyo Ibekunle Amosun bai damka musu cikon harsasai 780 da ke hannun sa ba.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Oyo, Bashir Makama ne ya bayyana wa Sufeto Janar Muhammed Adamu haka

Wannan zargi ya kara inganta tunanin da ake yi cewa Amosun bai damka wa ‘yan sanda dukkan makaman da ke hannun sa ba. Wannan ne kuwa jama’a da dama ke cewa sai fa an gudanar da kwakwaran bincike sannan za a iya ganewa.

Bayan da PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Amosun ya gina rumbun ajiyar makamai a Gidan Gwamnati a lokacin ya na gwamnan Ogun, da kuma yadda ya damka makaman a hannun Kwamishinan ‘Yan Sanda Makama, to a ranar 27 Ga Yuni kuma sai Makama ya rubuta masa wasika cewa – sun samu daya daga cikin akwatan da ke dauke da harsasan bindiga samfurin AK 47 a bude.

Cikin wasikar, Makama ya shaida wa Amosun cewa ya damka musu akwati 1,201 wadanda kowanen su ya na dauke da harsasai 1,200 na AK 47.

Ya kara da cewa amma kuma daya daga cikin akwatan “harsasai 420 kadai a cikin sa.”

A kan haka ne sai Kwamishinan ’Yan Sanda ya ce gaba daya harsasai 1,440,420 suka samu a cikin akwati 1,201, maimakon harsasai 1,441,200.

Sannan kuma Makama ya ce rigar sulke 271 suka karba a hannun Amosun da motar daukar jami’an tsaro daya.

Ya kara da cewa bai karbo AK 47 ko daya a hannun Amosun ba, saboda an rigaya an bai wa ‘yan sanda su tun cikin 2012.

INA SAURAN MAKAMAI SU KA SHIGE?

Duk da cewa rahoton da Makama ya yi, ya kusa daidai da ikirarin da Amosun ya yi cewa harsasai da riguna masu sulke da motar daurar jami’an tsaro kadai ya damka wa kwamishina gab da saukar sa mulki, amma kuma rahoton bai bayyana cewa Amosun ya damka wadannan bindigogi samfurin AK 47 ga ‘yan sanda a cikin 2012 ba.

Babu wasu wadatattun bayan da suka nuna cewa Amoun ya damka wa jami’an tsaro bindigogin tun a cikin 2012.

Abin da kawai rahoton ya ce shi ne an damka bindigar AK 47 guda 1,000 a hannun ‘yan sanda a ranar 20 Ga Yuli, 2012. Joseph Ameh na kamfanin Pointec Corporation ya damka bindigogin a madadin Amosun.

Sannan kuma Makama ya kasa yi wa Sufeto Janar bayanin dalilin da ya sa Amosun bai damka wa ‘yan sanda sauran tulin harsasai da riguna masu sulke ba, tun a cikin 2012, alhalin kuma duk a lokaci daya aka sayo su.

Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa mai yiwuwa Makama ya kasa yi wa Sufeto Janar cikakken bayanin ko wadancan bindigogi na 2012 na da alaka da wadannan sabbin da aka damka wa ‘yan sanda a 2019 ko kuma kowanne daban suke, saboda shi Makama sabon kwamishinan ‘yan sanda ne a Ogun.

“Ba mu sani ba ko Sufeto Janar sai bada umarnin a sake gudanar da kwakkwaran bincike.” Inji majiyar wadda ta san da batun harkallar makaman.

Kwamishinan ’Yan Sanda Makama ya ki amsa tambayoyin da PREMIUM TIMES ta yi masa a kan wannan harkalla. Ya ce duk wasu tambayoyi Amosun ne ya kamata a yi wa su, ba shi ba.

Shi ma kakakin yada labarai na Amosun, Mista Dorujaiye ya ki cewa komai.

Ita ma jam’iyyar APC ta yi kira a gudanar da kwakkwaran bincike a kan Amosun domin amfanin tsaron kasar nan, maimakon a ce an hana a bincike shi, saboda kusancin sa da Shugaba Buhari.

Share.

game da Author