HARE-HARE: Sojoji sun kashe mahara 5, sun kama 4 a dajin Kaduna

0

Sojojin Operation Harbin Kunama sun bayyana cewa sun kashe mahara guda biyar, sannan sun damke wasu 4 a cikin dazukan Karamar Hukumar Igabi, cikin Jihar Kaduna.

Kakakin Yada Labarai na rundunar mai suna Kanar Ezindu Idimali ne ya bayyana wa manema labarai haka a yau Lahadi a Kaduna.

Ya kara da cewa akwai kuma wasu da suka tsere da raunuka a jikin su, wadanda ya ce a yi kaffa-kaffa da su tare da gaggauta kai rahoton bakon-ido.

“An kai musu mamaki ne a ranar 24 Ga Yuli a Dagu cikin karamar hukumar Igabi. Kuma mun ceto wasu mutane biyu da suka yi garkuwa da su. Mutanen biyu su ne Malam Yakubu Hamidu da kuma Alhaji Isa Sa’idu.”

Ya ce sun samu nasarar kubutar da mutanen biyu wadanda aka yi garkuwa da su ne a Mahadar Makarfi Farm a ranar 25 Ga Yuli.

Kanar din ya ce an samu bindiga da sauran makamai da harsasai a hannun maharan. An kuma lalata musu babur guda daya a lokacin da sojojin ke bude musu wuta a dazukan ayyukan Kubuso, Kuso da Kakumi cikin Karamar Hukumar Igabi.

Babban Kwamandan Runduna ta Daya ta Kaduna, Faruq Yahaya, ya jinjina wa sojojin.

Share.

game da Author