Kungiyar Bada Jinkai ta Duniya, wato Amnesty International, ta yi tir da hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke na haramta IMN, wato Mabiya Harkar Islamiyya, masu goyon bayan Sheikh El-Zakzaky.
Ta ce bayyana IMN a matsayin ‘yan ta’adda da haramta su, tauye ‘yancin yin addini ne kuma tauye ‘yancin yin kungiya ne.
Kungiyar Harkokin Addinin Musulunci na (IMN) da wadda Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ke jagoranci ce aka bayyana a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda. Hakan ya faru ne tun bayan arangamar da mabiyan malamin suka yi da jami’an tsaro a Abuja, a ranar 22 Ga Yuli, har aka rasa rayuka, ciki har da na wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda da kuma dan jarida, a Abuja.
Duk da cewa mahukunta sun zargi mabiya Shi’a da alhakin kisan wannan dan sanda, Shi’a sun ce karya ake yi musu. Amma dai har zuwa lokacin rubuta wannan labari babu wata hujjar cewa mabiyan Shi’a masu zanga-zanga din ne suka harbe shi har wuri biyu a kan sa.
Ranar Talata ne Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu ya ce idan mabiyan Shi’a suka kara fitowa zanga-zanga, to a dauke su matsayi daya da ‘yan ta’adda.
Daga nan kuma ya bayar da umarnin duk inda aka gan su a damke su, su da shugabannin su.
Amma kuma Amnesty International, ta bayyana cewa: “ Haramta mabiyan El-Zakzaky wata manakisa ce domin a karkatar da kan jama’a daga rashin adalcin da aka yi na kashe mabiyan malamin sama da 350 a Zari’a, cikin Disamba, 2015, da kuma wasu wurare da dama.” Haka Kakakin Amnesty International, Isa Sanusi ya bayyana wa PREMIUM TIMES, jiya Talata da dare.
“Mambobin IMN da yawan gaske sun bace, iyalan su na ta neman su, ba a san halin da suke ciki ba. Sannan kuma gwamnati sai watsi ta ke yi da kokarin neman a yi musu adalci.”
Duk da umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar na a saki malamin domin ya je a yi magani shi da matar sa, gwamnati ta ki sakin sa, a bisa dalili na tsaro kamar yadda ta bayyana.