Har yanzu ana fama da kuncin talauci, duk kuwa da karin tattalin arziki – Oshiomhole

0

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa har yanzu akwai hauhawar kuncin talauci sosai a kasar nan, duk kuwa da cewa tattalin arziki ya karu.

Oshiomhole ya yi wannan tsokaci ne yayin da ya ke jawabi wurin taron Nazari Da Bitar Alkawurran Da APC Ta Cika a lokacin kamfen daga 2015 zuwa yau.

Taron wanda ya gudana a Fadar Shugaban Kasa, ya samu halartar jiga-jigan gwamnati kama daga Shugaba Muhammadu Buhari, gwamnoni da sauran su.

Oshiomhole ya ce ko shakka babu gwamnatin Buhari ta yi rawar gani sosai wajen kawo ci gaba a kasar nan, musamman idan aka dubi alkawurran da ta cika.

“Amma fa har yanzu dimbin jama’a na fama da kuncin talauci da kuncin rayuwa.” Inji Oshiomhole, kuma ya kara da cewa akwai bukatar bankuna su bude wuta da kara himma sosai wajen bayar da kananan basussuka ga matsakaitan masu sana’o’i, domin tattalin arziki ya inganta.

Ya kara da yin tsokacin cewa matsawar ci gaban da tattalin arzikin kasar nan ke yi bai haura gejin yawan haihuwar da ake yi a kasar nan ba, to za a ci gaba da daka tsalle ne kawai a wuri daya.

Bayanin sa ya yi kama da na Shugaba Buhari, wanda tun da farko ya bada bayanin yadda ya fitar da kasar nan cikin kuncin tattalin arziki a shekaru biyu da suka gabata.

A kan haka, shi ma Oshiomhole ya jaddada haka, har ya nuna cewa a fannin haka rashawa an samu ci gaba, idan aka dubi yadda kotuna ke wato kudade da kadarori a hannun jama’a.

Sai dai ya kara da cewa akwai bukatar a toshe wasu kofofin da kudaden gwamnati ke zurarewa, musamman daga tara haraji.

Ya ce gwamnatin APC a karkashin Shugaba Buhari ta samar da ci gaba sosai. Dalili kenan ma ake taron bitar, domin bibiyar alkawurran da aka cika daga cikin wadanda aka dauki alkawarin za a aiwatar a lokacin kamfen.

Share.

game da Author