HANA SA HIJABI: Iyayen dalibai Musulmi sun gargadi shugabar sakadaren ISI

0

Iyayen dalibai mata Musulmi na sakandaren International School Ibadan (ISI) da ke Jami’ar Ibadan, sun zargi shugabar makarantar Phebean Olowe da laifin ruruta wutar wani rikici a cikin makarantar ta hanyar kuntata wa dalibai mata Musulmi masu neman sai an bar su suna saka hijabi a cikin makarantar.

Kungiyar Iyayen Dalibai Musulmin na sakandaren ISI ce ta yi wannan zargi a ranar Asabar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Iyayen sun yi ikirarin cewa hukumar makarantar na kuntata wa dalibai mata Musulmi masu zuwa makarantar sanye da hijabi.

Tun a cikin watan Nuwamba, 2018 ne batun sanya hijabi ya zama rikici a makarantar, har ta kai ga kungiyar iyayen dalibai mata musulmi suka maka makarantar, Jami’ar Ibadan da kuma Hukumar Gudanarwar makarantar kotu.

Amma kuma a ranar 26 Ga Yuni, sai Babbar Kotun Jihar Oyo ta kori karar, a bisa dalilin cewa wadanda suka kai karar ba su da hurumin kai kara a kungiyance.

Sai kuma a ranar Alhamis da ta gabata ne wani wanda ‘yar sa ke karatu a makarantar, mai suna Idris Badiru, ya zargi Shugabar Makarantar Misis Olowe da Akantan makarantar Mista Odewale da wasu malaman makarantar da cewa sun ci zarafin ‘yar sa Ikhlas Badiru.

Badiru ya ce duka da kotu ta ce kungiya ba ta da ‘yancin kai kara, bai yiwuwa a hana ‘yar sa ‘yancin ta na yin shigar hijabi a makaranta.

Badiru ya bai wa PREMIUM TIMES labarin yadda a gaban sa aka hana ‘yar sa shiga makaranta sanye da hijabi a kofar shiga makarantar.

“Nan take na harzuka, rai na ya baci matuka, a matsayi na na uba, a gaba na aka danne wa ‘ya ta hakkin ta. Kuma abin haushi, matakarantar ta na cikin harabar ginin Jami’ar Ibadance, mallakin Gwamnatin Tarayya. Kuma wannan ne karo na biyu kenan da aka kuntata wa ’ya ta saboda ta sanya hijabi.

“Safiyar 4 Ga Yuli kuma na kai yara na makarantar, sai na samu gungun jami’an tsaro na Jami’ar Ibadan da kuma ‘yan sanda dauke da bindigogi a daidai wurin da suke hana masu hijabi shiga makarantar.

“Suka sake hana ‘ya ta shiga makaranta sanye da hijabi. Sai na kira Shugaban Jami’an Tsaron Jami’ar, wanda shi kuma ya jajirce cewa lallai sai ‘ya ta ta cire hijabin ta kafin a bari ta shiga makarantar.”

Shugaban Kungiyar Iyayen Dalibai Musulmi na sakandaren ISI, Abdur-Rahman Balogun, ya gargadi shugabar makarantar da kada ta kuskura ta haddasa rikici a makarantar.

Sai dai kuma shugabar makarantar ta ki bayyana wa PREMIUM TIMES yadda lamarin ya ke. Yayin da wakilinmu ya kira lambar ta, ya gabatar da kan sa cewa shi dan jarida ne, sai shugabar makarantar ta kashe wayar sa.

Sannan kuma wakilin na mu ya tura mata sakon tambayoyi ta hanyar tes a lambar wayar ta, amma har yanzu ba ta maida masa amsa ba.

Share.

game da Author