HAJJIN BANA: Aƙalla Alhazai 6,856 suka sauka garin Madina daga Najeriya

0

Aƙalla Alhazai 6,856 a ka yi jigila zuwa Madina daga Najeriya.

Maniyyata daga jihohin Kaduna, Kogi, Kwara, Legas da jihar Katsina aka riga akayi gaba da su.

Ofishin hukumar dake garin Madina ne ya fidda sanarwar ya na mai kira ga Alhazai da su rika zama a gidajen su saboda zafi da ake yi a ƙasar.

Shugaban masu kula da Alhazai na Hukumar Alhazai ta kasa, Abdulƙaɗir Mohammed ne ya bayyana haka a Madina inda ya gargaɗi Alhazan da zu riƙa zama a ɗaƙunan su maimaƙon gararamba domin ana ƙola ranan gaske a ƙasar Saudiyya.

Share.

game da Author