Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Lagos za ta maida wa kowane maniyyaci N141,000, kamar yadda Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCOM) ta ba da umarni.
Hakan ya biyo sake bin diddigin tsarin biyan kudaden tafiya aikin Hajji ne da aka yi wannan shekara, wanda hakan ya haifar da yin rangwamen da tilas sai an kowane maniyyaci an maida masa wasu adadin kudade daga cikin wadanda ya rigaya ya biya.
Wannan ramuwa da za a yi wa maniyyata, ta shafi na kowace jiha ce a fadin kasar nan, har da Abuja.
Amma bai shafi masu tafiya a jirgin yawo ba, wadanda aka fi sani da ‘yan ‘International’.
Ranar Laraba ne Jagoran Maniyyatan Jihar Lagos, Abdul-Lateef Abdul-Hakeem ya bayyana wannan garabasa ta naira N141,000 za a maida wa kowane maniyyacin jihar Lagos.
Ya yi wannan sanarwa ce a wurin taron wayar wa maniyyata kai da hukumar NAHCOM ta shirya wa maniyyatan Jihar Lagos.
“A wannan karo maniyyata sun biya kudi fiye da adadin da NAHCOM ta kayyade, dalili kenan za mu rama wa kowane wadannan adadin kudade da suka biya, domin sun yi yawa matuka.”
Ya ce wannan ya na nuna wa jama’a cewa gwamnatin Gwamna Babajide Sanya-Olu ba ta amince da harkalla ba ko kadan.
Ya ce jihar Lagos za ta maida wa maniyyatan ta kudade fiye da abin da kowace jiha za ta maida wa na ta maniyyatan, saboda kudaden da maniyyatan Lagos suka kara sun zarce na wadanda sauran suka kara nesa ba kusa ba.
Ya kuma yi alkawarin cewa maniyyatan Jihar Lagos za su yin santin irin kulawar da za su samu a lokacin wannan aikin Hajji na 2019.