HAJJI 2019: Hukumar Alhazai ta tura jami’ai 41 domin fara tarbar maniyyata

0

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta tura tawagar jami’ai 41 domin fara yi wa maniyyatan farko sharar hanyar shirye-shiryen isa Saudi Arebiya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Jami’an wadanda suka tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja, sun isa Saudi ne domin shirin fara daukar maniyyata daga Najeriya zuwa Saudi Arebiya.

Da ya ke musu jawabi, Shugaban Hukumar Alhazai, Abdullahi Muhammad, ya hore su da su zama masu nuna halaye na kwarai tare da tabbatar da samun nasarar aikin Hajjin 2019.

“Yanayin dabi’un ku da aikin ku tukuru da kamun kan ku da mu’amalar ku duk sun a da tasiri kwarai. Kuma duk za a yi amfani da su wajen auna nasarar da mu ka samu yayin gudanar da aikin Hajjin bana.”

Daga nan sai ya kara tuna wa jami’an cewa su tuna sun je ne dokin gudanar da ayyukan kasar su. Don haka su tabbatar cewa sun zama wakilai kuma jakadu nagari.

Ya kuma kara sanar da su cea su tabbatar da dukkan maniyyata sun ji dadi, kuma an kula da walwala da dawainiyar su. Domin kamar yadda ya ce, idan da babu wadannan maniyyata, to su jami’an ba za a tura su har su je su wakilci kasar nan ba.

Sai kuma ya kara bayyana musu cewa su gode Allah da har aka zabe su kuma aka tura su kasa mai tsarki domin su je su yi wa Alhazai hidima.

A karshe ya gargade su cewa su tabbatar su bada goyon baya da hadin kai ga jami’an Saudi Arebiya, domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.

Share.

game da Author