HAJJI 2019: Hukumar Alhazai ta nada jami’an kula da kowane masaukin Alhazai

0

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta nada jami’an kula da kowane otal-otal da za ta saukar da maniyyatan Najeriya a Madina.

Babban Jami’in Kula da Mahajjatan Najeriya a Madina, kuma Sakataren Riko na NAHCON, Ahmad Maigari ne ya yi wannan sanarwa a lokacin da ya gudanar da taro da masu ruwa da tsaki wajen samar da mazaukai a Madina.

Ya ce wannan sabon tsarin da aka fito da shi zai samar da yanayin gudanar da ayyukan kula da mahajjata a cikin gaggauwa, kai musu dauki nan da nan da kuma biya musu dukkan bukatun dawainiyar su.

Kamar yadda ya kara yin bayani, ya ce wannan tsari zai kuma kara samar da hanyoyin sadarwa da tuntubar juna ga daukacin masaukan Alhazan Najeriya da kuma kan su ma’aikatan da jami’an NAHCON baki daya a lokutan gudanar da aikin ziyara a Madina.

Kamar yadda tsarin tafiya aikin Hajji ya ke, wadanda aka fara jigila daga farko-farko, su na zarcewa ne Madina su fara yin kwanakin ziyarce-ziyarce a can, kafin a wuce da su Makka.

Bayan kammala aikin Hajji kuma, sai a kwashe su daga Makka zuwa filin jirgin Jedda, domin maido su gida Najeriya.

Maigari ya ce an gudanar da taron ne tare da masu mazaukan bakin domin tabbatar da cewa an samu hanyoyi nagari wajen kula da jin dadin Alhazan Najeriya.

Wannan kuma inji shi ya sa NAHCON ta gani da idon kuma ta ji irin shirye-shiryen da aka rigaya aka samar a kasa domin kula da Mahajjatan Najeriya.

Ana sa ran jirgin farko daga Najeriya zai tashi ne daga Katsina, inda zai fara kwasar Maniyyatan shiyyar Dutsinma.

Share.

game da Author