Akalla maniyyata 1,529 ne suka fara tashi daga Najeriya zuwa kasar Saudiyya a jigilar Alhazai da aka fara daga Najeriya.
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da haka a shafinta ta tiwita.
Bisa ga sanarwar maniyyata daga jihar Kaduna 542 ne suka tashi zuwa Madinah a jirgin saman kamfanin Medviwe da karfe 8:02.
“Jirgin saman ta kwashi maza 348 da mata 194.
“Daga jihar Legas jirgin saman Flynas ne ya kwashi maniyyata 432 da karfe 1:11 na rana.
“Sannan daga jihar Kano jirgin saman MaxAir ne ya kwashi maniyyata 555 wanda a ciki akwai ma’aikatan NAHCON 10.
“Jirgin ya kwashi maza 315 da mata 240 da karfe 1:55 na rana”.
Idan ba manta ba Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta tura tawagar jami’ai 41 domin fara yi wa maniyyatan farko sharar hanyar shirye-shiryen isa Saudi Arebiya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Jami’an wadanda suka tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja, sun isa Saudi ne domin shirin fara daukar maniyyata daga Najeriya zuwa Saudi Arebiya.
Jami’an za su tabbatar da dukkan maniyyata sun ji dadi, kuma an kula da walwala da dawainiyar su.
Sannan kamata ya yi jami’an su hada hannu da jami’an kasar4 Saudu domin ganin hakan ya faru.
Discussion about this post