Maniyyata tafiya aikin Hajjin 2019 a fadin jihohi 6 da Abuja, za su fuskanci wasu abubuwa guda 8, kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana.
Jami’ar Yada Labarai ta NAHCON, Fatima Usara ce ta bayar da wannan karin haske a jiya Litinin a Abuja.
Sannan kuma ta shawarci maniyyatan cewa idan sun je kasar Saudiyya, to ya zama wajibin su da su kame kan su tare da nuna da’a a kasa mai tsarki.
Ta ce a cikin wannan mako na farkon watan Yuli ne za a fara jigilar maniyyata zuwa Saudiyya daga kasashe daban-daban na fadin duniya.
NAHCON na sa ran maniyyata daga Najeriya za su fara tashi daga ranar 10 Ga Yuli, 2019.
ABUBUWA 8 DA MANIYYATA ZA SU FUSKANTA
1. Duk wanda ya san ya kammala biyan kudin aikin Hajji gaba daya, to ya sa ran karbar naira 51,000 da aka yi wa kowa ragi daga cikin kudin kujerar bana. An ware naira bilyan 3.326 domin biyan wadannan kudaden ragi da aka yi wa maniyyata.
2. Maniyyata za su fuskanci binciken tantancewa daga jami’an jami’an shige-da-fice na Saudiyya (immigration), tun daga nan Najeriya, daga filayen jiragen sama da za su tashi.
A karkashin wannan tsari, tun daga wurin shiga jirgi a nan Najeriya kowane maniyyaci zai rabu da jakar sa. Sai dai ya karbi abin sa a dakin otel din da aka saukar da shi ko a Makka ko a Madina. Wanan zai kawar da matsalar cusa wa maniyyata kwayoyi a cikin jaka ba tare da sanin su ba. Kuma zai rage tsawon bata lokacin da ake yi kafin a bar filin jirgin Jedda idan an sauka.
3. Masana tsaro sun tabbatar da cewa baya ga lokutan gudanar da zabe a kasar nan, lokacin tafiya aikin Hajji ne ya fi zama jami’an tsaro kan fuskanci babban kalubale a kasar nan.
A wannan lokuta ne ake samun dimbin jama’a na gudanar da ayyuka a lokaci daya. Kuma ta nan ne batagari kan samu damar gudanar da mugun nufin su.
Saboda hakkin gwamnati ne kare al’ummar kasar ta da kuma damke batagari, maniyatan Najeriya za su fuskanci tsatstsauran binciken kwakwaf a wannan lokacin tafiya aikin Hajji.
Za a tsaurara kula da maniyyata a sansanin mahajjata da kuma sansanonin jiran tashin Alhazai domin a hana mutane karakaina a cikin maniyyata. Musamman gudun kada a rika shiga ana damfarar maniyyatan da suka fito daga karkara.
Maniyyata Hajjin bana su guji zuwa sansanin Alhazai da dimbin ’yan rakiya. Domin ba za a bar su su shiga ciki ba.
Maniyyata su rika gaggautawa su na kai rahoton duk wani bakon-idon da ba su amince da shi ba, ko kuma ya yi kokarin damfarar su. Sannan kuma su rika bincikawa daga jami’an su idan suka ji ana watsa ji-ta-ji-ta.
4. Kada maniyyata suka kiran masu tallar kayayyaki su na matsar kusa da shingen waya ko bangfon da aka killace su.
An bada umarnin yadda za a rika gudanar da dawainiyar maniyyata a sansanin Alhazai domin hana matasa ’yan bankaura shiga cikin su da sunan taimakon su.
Har a biranen Makka da Madina za a rika amfani da jami’an tsaro su na sa-ido a kan mahajjata, bisa la’akari da abubuwan da suka rika faruwa a lokacin aikin Hajjin da ya gabata na shekara ta 2018.
A kowane masauki a Madina misali, za a ajiye Manajan Kula da Gida, wanda zai lika lambar wayar sa a babban falon gidan (reception). Wannan lambar ce duk mai bukatar dillalan canjin kudi gangariya zai tambaya, kuma za a sanar da shi. Idan ma akwai mai wata tambaya ko neman karin haske ko wata cigaya, to wannan lambar zai tuntuba.
Wannan Manajan Masaukin Alhazai zai rika kula da kuma tabbatar da cewa rubdugun Tikari ba su ruka shiga cikin otal-otal ko masaiukan kai-tsaye ba.
Don haka ana bai wa mahajjata shawara kada su rika shigar da Tikari cikin gidajen da aka saukar da su, ko cikin dakunan su. Domin yin hakan kasada ce babba.
Akwai kuma lambar isar da korafe-korafe ga Hukumar Alhazai ta Najeriya idan an isa Saudiyya: +966920008251.
5. Ko a wajen tafiya daga nan ko kuma wajen dawowa a daga filin jirgin Jedda, to mahajjaci ya kwana da shirin cewa za a dauki tsawon lokaci ana bincike kafin a shiga jirgi a tashi.
A Saudiyya idan aka kira mutane su je filin jirgi, to za a iya shafe kwana daya cur a wurin bincike kafin a kammala har a taso a nufo gida Najeriya.
Haka ma nan a Najeriya, idan an kira maniyyata, za su iya kwashe kwana daya cur, wato awa 24 kafin a kammala bincike har jirgi ya tashi.
Idan aka hadu da rincimi daga bangaren maniyyata, to za a iya dakatar da binciken tantancewa har sai kowa ya natsu tukunna.
6. Idan aka fara aikin Hajji ka’in-da-na’in, ana bukatar Mahajjata daga Najeriya su jira umarni ko sanarwa daga jami’an sun a jihohin su, domin sanar da su lokutan da za su je su yi jifar Shaidan da kuma dawafi.
Jami’an kasar Saudiyya sun bayyana cewa za a takaita tare da kafa ka’idoji a wajen jifa, domin a magance cinkoson maniyyata a wurin jifa da dawafi.
7. Mahajjatan Jirgin Yawo kuwa za a dan kara cajin su wasu ‘yan kudin tafiya Makkah ta jirgin kasa. Musamman daga Madina ga wadanda suka fara tafiya aikin Hajji daga karshe-karshe.
8. A karshe ana sa ran cewa tsarin abincin ciyarwa da ‘yan Najeriya da aka yi zai burge su kuma ya gamsar da su.
Za a rika shirya wa mahajjata hadadden abinci kala daban-dadan, wanda aka shirya wannan tsari tare da jami’an kasar Saudiyya.
Amma kuma duk wanda bai ji dabin abincin da aka ba shi ba, to zai iya kai kuka a bangaren jihar da ya ci abincin.