HADARIN MOTA: Mutum daya ya rasu, wani ya ji ciwo a jihar Kano

0

A hanyar Rano, karamar hukumar Bunkure dake jihar Kano ne tankar mai ta kama da wuta inda mutum daya ya rasu sannan wani ya sami rauni a jikin sa.

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Saidu Mohammed ya sanar da haka.

Mohammed yace wannan abin tausayin ya faru ne ranar Alhamis da karfe 8:52 na safe.

Ya ce tankin man ta kama da wutane saboda cike take da bakin mai ‘Diessel’. Sannan ana zaton cewa tukin ganganci da wauta na direban tankin ne sillar haddarin.

“ Wani Malam Mohammed ne ya kira mu ta wayar tarho ya sanar mana da abin da ya faru daga nan ne muka gaggauta zuwa wajen.

“Mun gano cewa Malam Danladi, mai shekaru 45 da Abubakar Ya’u, mai shekaru 35, ne ke cikin wannan mota.

A karshe ya yi kira ga direbobi da su rika tuki da kula sannan su daina yin ganganci a hanya.

Share.

game da Author