Gidauniyar Bill da Melinda Gates ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta maida hankali wajen kawo karshen cutar Shan-inna

0

Gidauniyar Bill da Melinda Gates ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta maida hankali wajen kawo karshen cutar Shan-inna.

Jami’in gidauniyar Mark Suzman ne ya yi wannan kira da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

Suzman yace kamata ya yi gwamnatin kasar nan ta yi kokarin ganin an yi wa kowani yaro allurar rigakafin cutar.

“Wild Virus wani irin cutar shan inna ne dake shanye bangaren jiki.

“Bayanai sun nuna cewa Najeriya ta yi kusan shekaru uku rabon da ace wai an samu labarin wani da ya kamu da cutar a kasar nan. Bullowar cutar a jihar Barno ya hana kasar nan samun satifikat din rabuwa da cutar kwata-kwata daga kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO).

A karshe Suzman ya ce gidauniyar za ta tallafa wa sauran bangarorin kasar kamar su aiyukkan noma bayan ta kammala da yaki da kawar da shan inna.

Share.

game da Author