Fadar Shugaban Kasa ta yi magana dangane da halin da rayuwar ma’aikatan agajin da Boko Haram suka garkuwa da su ke ciki.
An yi garkuwa da su ranar Alhamis, kwanaki 8 da suka gabata yayin da su shida da ke aiki a karkashin Kungiyar Action Against Hunger suka fada hannun Boko Haram.
An nuno su a wani faifan bidiyo inda daya daga cikin su ke rokon cewa a ceci rayuwar su, kada gwamnati ta bari a kashe su, kamar yadda aka kashe wasu ma’aikatan agaji a baya.
Bidiyon mai tsawon minting 3 da sakan 17, ya nuna mace daya daga cikin sauran mazan biyar mai suna Grace ta na magana da harshen Turanci, inda ta ke rokon gwamnatin tarayya kada ta bari a kashe su.
A martanin da Fadar Shugaban Kasa ta fitar jiya Alhamis da dare, ta ce ta damu kwarai dangane da wannan bidiyo, wannan daya daga cikin hukumomin tsaron kasar nan ya sanar da gwamnatin tarayya.
“Fadar Shugaban Kasa na tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da tattaunawar tuntubar wadanda suka yi garkuwa da su.
“Banda wa su wadannan ma’aikatan jiyya su shida, akwai wadanda ake tattauna maganar sakin su, ciki har da Leah Sheribu. Kuma akwai wani malamin addini da sauran su.
“Dama tuni ake tattaunawa, amma batun wadannan ma’aikatan agaji ya kara zaburar da kokarin da jami’an sirri ke yi domin ganin nasarar tattauna kubutar da su.
Gwamnati ta ce ta na fatan kada wadanda suka yi garkuwar da su dai su yi musu wata illa kafin a cimma karbo su.
Garba Shehu, Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa ne ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya fitar jiya Alhamis da dare.
FASSARAR ROKON DA GRACE TA YI WA GWAMNATI:
“Suna na Grace, Ina aiki da Kungiyar Agaji ta Action Against Hunger, a Jihar Barno. A Damasak ne ofishin gudanarwar kungiyar ya ke.
“Mun je aiki ne a Damasak a ranar 18 Ga Yuli, 2019, to a kan hanyar mu ta komawa Damasak, sai mu ka ci karo da sojojin Khalifa, suka kama mu. Sai suka kawo mu nan. Kuma a gaskiya ba mu san ko ma ina ba ne nan din.
“Amma a wannan lokaci, ina roko ha Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), saboda ni kadai ce Kirista.
“Ina rokon CAN ta gaggauta yin wani kokari dangane da ceton rayuwa ta. Ina kuma rokon Action Against Hunger a Jihar Barno, cewa mu shida ne ma’aikatan su da aka kama, kuma duk ga mu nan a tsare.
“Ina rokon Action Against Hunger su sani cewa mu na da vitali, wasun mu su na ma da ‘ya’ya. Don haka su yi wani kokari domin ceto rayuwan mu.
“Ina kuma yin kira ga Najeriya cewa ta tuna mu ma fa ‘yan Najeriya ne, kuma Najeriya mu ke wa aiki. Ina rokon gwamnatin Najeriya ta yi kokarin ganin t ceci rayuwar mu.
“Saboda irin haka ta faru ba ma’aikatan RED CROSS, inda inda wasu mata Hauwa da Kabura aka kashe su, saboda Najeriya ba ta maida hankali wajen ganin an nemi a sake su ba.
Ina roko a madadin sauran mu da ke nan a tsare, kada Najeriya ta bari a yi mana irin kisan da aka yi wa Hauwa da Kabura. Irin haka kuma ta faru ba Leah da Alice -saboda Najeriya ta kasa yin komai a kan su.
“Ina kara yin roko ga Najeriya da Action Against Hunger su gaggauta ceto mu.”
Na gode.
Discussion about this post