Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa Shirin Gina wa Fulani Makiyaya Rugage, ba wai Fulanin ne kadai za su ci gajiyar shirin ba.
Ganin yadda jihohi da kabilu da dama cikin kasar nan ke nuna rashin amincewa da kafa wa Fulani rugage a cikin yankunan su, wannan ya sa Fadar Shugaban Kasa ta fito ta yi karin haske a jiya Lahadi.
A kan hana ke Kakakin Yada Labarai na ShugabaMuhammau Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa hatta su ma sauran masu kiwon wasu dabbobin daban, duk za su ci moriyar shirin kafa rugagen.
“Rugagen da gwamnati ke kokarin kafawa, za ta gina su ne domin samar wa makiyaya masu tashi daga nan zuwa can matsuguni wuri guda. Za su zauna ne a wuraren da za su iya samun damar yin kiwo, ga asibiti, ga makarantu, ga kasuwanni da sauran ababen jin saukin gudanar da rayuwa kamar hanyar zirga-zirgar motoci.
“Babban alfanun wannan shiri dai zai kasance rage yawaitar fadace-fadacen makiyaya da manoma.” Cewar Shehu.
Ya ce gwamnati na kokarin kawo karshen yadda ake gudanar da kiwon dabbobi barkatai, wanda hakan kan haifar da rikice-rikice a cikin al’umma.
“Idan aka gina rugagen, shi kan sa naman dabbobi za a fi samun saukin tsaftace shi, sannan kuma za a kara samun yawaitar madara ko kindirmo sosai, ta yadda harkar kindiromon zai zama babban kasuwanci. Kuma tsarin kiwo zai inganta.”
Hakan kuma a cewar Shehu, zai samar da aikin yi, samar da lamuni ga masu sana’a da masu kiwo, samar da tsaro ga iyalan makiyaya da kuma dakile satar shanu.
Shehu ya kuma yi kira da a daina saka siyasa cikin lamarin, domin babu inda gwamnatin tarayya za ta tilasta wa jihohi sai an gina rugage, kuma gwamnatin tarayya ba ta ce za ta kwace wa manoma gonaki ta gina rugage ba.
Ya zuwa yanzu dai jihohi 12 ne suka nuna bukatar kafa wa makiyaya rugage a cikin su.