FADAN KAWAYE: Zainab ta guntule wa Jummai yatsa da cizo a Kaduna

0

Kotun gake Magajin Gari, Kaduna ta gurfanar da Zainab Mohammed dake zama a Titin Kano Road a cikin garin Kaduna bisa kiran kawarta da sunayen banza sannan kuma ta yi mata dukan tsiya har da guntule mata yatsa da hakora.

Alkalin kotun Murtala Nasir ya bai wa Zainab damar ta biya kudin beli da gabatar da shaidan da zai biya Naira 70,000 a kotun.

Nasir ya dage shari’ar zuwa ranan 23 ga watan Yuli domin kawar da aka ciza ta samu lafiya tukunna.

Yayin da kotun ta zauna lauyen da ya shigar da karar Aliyu Ibrahim ya bayyana cewa Jummai Babangida dake zama a Titin ‘Katsina Road’ ce ta kawo karar a ofishin ‘yan sanda dake Magajin Gari bayan abin ya faru.

Ibrahim yace Jummai ta bayyana wa ‘yan sanda cewa haka kawai a ranar 7 ga watan Yuli da karfe takwas na safe Zainab wacce ‘yar kasuwa ce ta gamu da ita a hanya ta kawai sai ta hauta da duka acikin haka ne fa ta kama hannayenta ta guntule da cizo.

“Jummai ta ce Zainab ta kira ta maiya, ta ji mata rauni a jiki sannan ta yi mata kashejin cewa daga ranan kada ta yadda su yi ido hudu kuma, domin duk inda suka hadu sai ta sake narkarta.”

Share.

game da Author