Dole mu maida hankali wajen gamawa da ‘Yan ta’adda – Buhari

0

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce daga yanzu mahara su sani cewa gwamnati ba za ta yi musu da sauƙi ba ganin yadda hare-hare yaƙi ci yaƙi cinyewa a ƙasar nan.

Buhari ya nuna matuƙar rashin jindadin sa game da harin da aka kai garin Goronyo ranar Juma’a inda aka kashe aƙalla mutane 37.

A takarda da aka fitar daga ofishin shugaban ƙasan wanda Kakakin sa Garba Shehu ya saka wa hannu.

Buhari ya jajanta wa mutanen Goronyo da gwamnatin jihar Sokoto bisa abinda ya faru.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da Sarkin Musulmi Saad Abubakar duk sun ziyarci ƙauyukan da aka kai harin.

Tuni dai har an ƙara tura tulin dakaru zuwa wadannan garuruwa domin samar da tsaro.

A ranar Juma’a ne wasu ’yan bindiga suka kai hare-hare a cikin wasu kauyukan da ke karkashin Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane 37.

Wani mazaunin Goronyo mai suna Shafiya’u, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an bar gawarwakin wadanda aka kashe zube, saboda jama’a da kuma jami’an tsaro ba su iya shiga lungun da aka yi kisan da wuri ba.

“An fi kashe jama’a da dama a kauyen Kamitau, saboda al’ummar garin sun yi gangami su ka bi mahara a guje da nufin kwato shanun su da aka kwace. Amma kuma sai aka samu akasi, da suka kure wa ‘yan bindigar gudu, sai suka bude musu wuta, har suka yi musu mummunan kisa.’ Inji Shafaya’u.

Wata majiya ta ce masu harin sun dira wajen karfe 5 har zuwa 7 na dare. Kuma sun hakkake cewa daga cikin Jamhuriyar Nijar su ka shigo.

Limamin masallacin Izala na Goronyo, Isma’il Sani, ya yi kira a lokacinn hudubar sa ta ranar Juma’a cewa gwamnati ta tashi tsaye domin ta hana sake zubar da jinin jama’a haka nan.

Share.

game da Author