DAUKAR FANSA: Yadda Boko Haram suka kashe ‘yan zaman makoki 60 a Barno

0

Al’amarin wannan mummunan kisa ya faru ne Asabar da ta wuce da dare, a wani kauye da ake kira Badu, wanda ke a karkashin Karamar Hukumar Nganzai, cikin Jihar Barno.

Boko Haram ne suka yi wa mazauna zaman makoki dirar mikiya a cikin mummunan shiri, suka bude musu wuta, har suka kashe mutane 60, sannan kuma wasu 11 suka ji mummunan raunuka.

Jami’ai a Karamar Hukumar Nganzai sun tabbatar da cewa harin daukar fansa ne Boko Haram suka kai kauyen, domin makwanni biyu da suka gabata, Boko Haram sun kwashi kashin su a hannun mutanen kauyen.

YADDA BOKO HARAM SUKA SHA RAGARGARA A KAUYEN BADU

Makonni biyu da suka gabata, Boko Haram suka kai kauyen, domin makwanni biyu da suka gabata, Boko Haram sun kwashi kashin su a hannun mutanen kauyen.

Jama’ar garin ba su tsorata ba, sai suka yi gagarimin shiri, suka tunkari Boko Haram har suka kashe ‘yan ta’adda 11 kuma su ka kwato bindigogi samfurin AK47 guda 10 daga hannun su.

Da yawan ‘yan Boko Haram da suka arce a lokacin, sun gudu da raunuka a jikin su.

Wannan abu bai yi wa Boko Haram dadi ko kadan ba. Su ma sai suka sake shiri, suka darkaki kauyen ranar Asabar da ta gabata.

Sun kai farmakin ramuwar-gayya a daidai lokacin da ake zaman makokin wani mamaci, inda suka mamaye masu makokin da harbi, har sai da suka kashe mutane 60, suka ji wa 11 rauni.

Shugaban Karamar Hukumar Nganzai, Muhammad Bulama, ya shaida wa manema labarai cewa harin kisan gillar na daukar fansa ne.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da Gwamna Umara Zulum ya kai ziyarar ta’aziyya da gani da ido a kauyen.

“Makonni biyu da suka gabata ne Boko Haram suka kai hari kauyen, amma sai mutanen garin tare da ‘yan sintiri suka jajirce, suka kashe mahara 11 kuma suka kawace musu bindigogi 1o kirar AK47.”

A halin yanzu dai wadanda suka ji ciwo na can ana kula da su a Babban Asibitin Maiduguri.

Gwamna Zulum ya yi wa mutanen kauyen jaje da ta’aziyya, ya kuma nuna bakin cikin sa dangane da faruwar mummunan al’amarin.

Share.

game da Author