Ranar 24 Ga Yuli, wasu mutane uku sun garzaya Kotun Koli, inda suka sake jajjada dalilan su na kalubalantar sahihancin takarar shugabancin kasa da jam’iyyar APC ta tsaida Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Kalu Kalu, Labaran Ismail da Hassy Kyari el-Kuris sun ce su na nan a kan bakan su cewa Buhari bai cancanci tsayawa takara ba. Don haka sun garzaya Kotun Koli ne domin a cewar su, ba su gamsu da hukuncin da Alkalin Kotun Daukaka Kara ya yanke, inda ya ki sauraren karar da suka shigar ba, kawai ya yi watsi da ita.
Bukatar su a Kotun Koli
Su na so Kotun Koli ta tabbatar wa duniya cewa Mai Shari’a na Kotun Daukaka Kara, Mohammed Idris ya tafka kura-kurai a hukuncin da ya yanke na kin sauraren karar su.
Sun nemi Kotun Koli ta tabbatar da cewa Buhari ya kantara karya a cikin fam din neman tsayawa takara mai lamba 001 da ya cike ya aika wa INEC.
Sun nemi Kotun Koli ta bayyana cewa soke takara ne hukuncin wanda ya kantara wa INEC karya a cikin fam mai lamba 001, kamar yadda doka ta shimfida.
Su na so Kotun Koli ta hana Buhari kiran kan sa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 23 Ga Fabrairu da ya gabata.
Sun nemi Kotun Koli ta umarci APC cewa kada ta kara kiran Buhari dan takarar ta na zaben 23 Ga Fabrairu.
Su na so Kotun Koli ta umarci INEC ta cire sunan Buhari daga jerin sunayen ‘yan takarar zaben shugaban kasa na 23 Ga Fabrairu.
Sun kuma nemi Kotun Koli ta bayyana wa duniya kuskuren da Babbar Kotun Tarayya ta Tafka inda ta fara ba korar karar su a bisa dalilin rashin shigar da karar cikin lokaci.
Uzurin su a Kotun Koli
Babban Lauya Ukpai Ukairo wanda ke wakiltar mutanen uku, ya gabatar da uzurin sa a Kotun Koli cewa:
Babbar Kotun Tarayya da Kotun Daukaka Kara sun kori karar su a bisa dalilin cewa sun shigar da karar bayan kwanakin wa’adin da ya kamata mai korafi a kan zabukan fidda-gwani na jam’iyya ya shigar da karar rashin amincewa da zabe sun shige.
Lauyan su mai suna Ukairo ya rattaba wa Kotun Koli cewa Babbar Kotun Tarayya da Kotun Daukaka Kara sun ki fahimtar cewa su karar da su ka shigar, ba ta da nasaba da wani rikici ko ja-in-ja da zaben fidda-gwanin APC na shugaban kasa ko wani korafi ga tsaida Buhari da APC ta yi.
Sun ce su jayayyar su ta tsaya ne kacokan a kan karyar da su ka ce Buhari ya kantara wa INEC a cikin fam mai lamba 001. Suka ce rantsuwar da ya yi a cikin fam din, wato ‘affidavit’, ta zama rantsuwar kaffarar kwansitution, wadda kaffarar da ta wajaba a kan Buhari, ita ce a soke takarar sa kawai.
Don haka sai Ukairo ya nuna cewa wa’adin da Dokar Kasa Sashe na 285 (9) ya gindaya cewa kada mai jayayya da zaben fidda-gwani ya wuce kwanaki 14 bai shigar da kara ba, ba ta hau kan su ba. Saboda su ba saboda zaben fidda-gwani ya tsaida Buhari su ka shigar da kara ba.
Sun shigar da kara ne a kan gundarin karyar da su ka ce Buhari ya tafka dangane da satifiket na kammala sakandare, a cikin fam din da ya cire, ya aika wa INEC.
Da ya koma kan batun wa’adin kwanaki 14 da ya kamata a ahigar da kara, lauya Ukairo ya rubuta wa Kotun Koli cewa mai shari’a a Babbar Kotun Tarayya bai yi amfani da ranar da suka shigar da karar ba, sai ya yi amfani da ranar da jami’an kotun suka shigar masa da karar a gaban sa. Sun kara da cewa Rajistara na Babbar Kotun Tarayya ne ya ki sa hannu da wuri a kan takardar karar da suka shigar.
Idan ba a manta ta, mutanen uku sun garzaya Kotun Koli ne, bayan Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da karar ta su a ranar 12 Ga Yuli.
Daga cikin abin da shi ma dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ke kalubalanta a kotu, har da rashin cancantar Buhari tsayawa takara a bisa dalilin abin da shi ma ya kira karyar da Buhari ya kantara wa INEC ta satifiket din sakandare.
Sai kuma magudin da shi da PDP su ka ce an yi a lokacin zaben.