Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, yam aka daya daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari kotu, inda ya nemi ta biya shi diyyar naira bilyan 2.5, domin ya sayi sabulun wanke kashin-kajin da ta goga masa, da sunan sa da ta bata a idon duniya.
Atiku ya nemi kotu ta tilasta wa Lauretta Onochie ta ta ba shi hakuri dangane da labaran karairayi da kango-kuregi wadanda ya ce Lauretta ta yi masa a shafin ta na Twitter da kuma Facebook.
Lauretta dai ta na daya daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari a kafafen yada labaru.
Atiku ya shigar da karar a ranar 26 Ga Yuni, bayan da ya bai wa Lauretta wa’adin wasu kwanaki ta ba shi hakuri tare da kuma karyata kanta da kan ta a kafafen yada labarai.
Ya ce ta buga karyata kan ta da kuma ba shi hakuri a manyan jaridu uku na kasar nan, da kuma shafin ta twitter da na Facebook, inda ta buga labaran karya a kan sa.
Lauretta dai ta buga cewa jami’an tsaron kasar Hadaddiyar Daurar Larabawa ( Dubai) sun sa masa ido, su na lura da irin yadda ya ke mu’amala, saboda zargin sa da mu’amala da masu tayar da zaune tsaye na cikin duniya.
Cikin inda Atiku ya kara neman ta buga neman afuwar sa, tare da karyata kan ta da kan ta, har da gidan talbijin na NTA na Kasa da kuma Gidan Talbijin na Channels.