Dakatar da KEDCO zai jefa sassan Kano cikin duhu na tsawon kwakani da dama

0

Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ya bada sanarwar dakatar da Kamfanin Saida Wutar Lantarki na ‘Kano Electricity Distribution Company’, wato KEDCO, a bisa dalilin kauce wa bin ka’idoji na tsawon lokaci da KEDCO din ke yi.

Jiya Lahadi ne aka bada sanarwar, wadda hakan ko shakka babu zai jefa yankunan Jihar Kano da dama a cikin duhu na tsawon kwanaki masu dama.

A cikin sanarwar dai TCN ya ce an dakatar da KEDCO daga karfar wutar lankarki daga TCN ta na sayarwa har sai yadda hali ya yi.

Sannan kuma sanarwar ta tabbatar da cewa tuni ma har an katse wasu taransifa da daman a KEDCO din daga karbar wuta a tashashon tattara wutar lantarki ta kasa.

An dakatar da KEDCO, wanda shi kadai ne kamfanin saida hasken lartarci a Kano saboda abin da TCN ya kira karya ka’idoji da yarjejeniyar huldan kasuwanci da KEDCO din ke ci gaba da yi duk kuwa da yawan gargadi da aka sha yi masa.

TCN ya ci gaba da cewa bayan an tura wa KEDCO takardar gargadi a ranar 9 Ga Yuli, an sake kara tura wata kuma a ranar 15 Ga Yuli, amma duk kamfanin bai warware matsalar ba.

A karshe dai ranar 19 Ga Yuli sai aka kafa kwamitin mutane uku da za su zauna su tuhumi KEDCO.

Sai dai kuma KEDCO bai tura shugabannin ta ko wakilai da zai wakilci kamfanin a wurin zaman kwamitin ba. sannan kuma bai aika dalilan da ya hana jami’an kamfanin kin halartar zaman kwamitin binciken ba.

Wannan kuwa inji TCN, to KEDCO ta karya Dokar Tsarin Kasuwancin Hasken Lantarki ta 45.3.9.

Daga nan sai TCN ya bada umarnin ya yanke wa KEDCO da ake bai wa kamfanin wutar lantarki na wasu sassa, har sai lokacin da ya warware matsalar sa tukunna.

Cikin tashoshin da aka yanke wa KEDCO wuta har da tashar wuta ta Kofar Dan’Agundi da ke cikin Kano.

Kwanan nan an yanke wa wasu Kafanonin Saida Wutar Lantarki wuta a Ikeja da ke Lagos, Enugu da kuma Benin.

Share.

game da Author