Dagargajewar da yankin Arewa ta yi, yayi daidai da Kasar Afganistan da tayi shekaru tana fama da yake-yake – El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa irin dagargajewar da yankin Arewa ta yi ya kai amisaltata da kasar Afganistan da ta yi ta fama da yake-yake shekaru da dama.

El-Rufai ya kara da cewa baya ga ci baya da yankin tayi wajen harkar Ilimi, ta fi kowacce yanki a kasar nan zama koma baya wajen kula da kiwon lafiya jama’ar yankin.

Sannan kuma yace kasashe biyu ne a Najeriya, da yankin Kudu da ta ci gaba da kuma yankin Arewa da ta ragwargawbe babu ci gaban da za a iya tunkaho da shi.

” Dole mu rika gaya juna gaskiya, a bisa lissafi da kididdigan masana, lalacewar da yankin Arewa tayi daidai yake da kasar Afganistan da ta dade ta fama da yake-yake.

” Najeriya ce ta fi yawan talakawa a duniya kuma mafi yawansu sunna yankin Arewa ne, Najeriya ce tafi yawan yaran da basu zuwa makaranta kuma dukkan su kaf suna yankin Arewa ne.

” Yanzu fa yankin Arewacin Najeriya ta zama cibiyar mashaya muggan kwayoyi, dandalin ‘yan iska, Barayi, Masu Garkuwa da Mutane, ‘yan ta’adda, yankin da ake fama da lalacewa da tabarbarewar auratayya da sauransu.

Baya ga haka ya musanta cewa da ake yi wai yankin Arewa bata amfanar kasa Najeriya da komai sai dai ci daga baitul malin da wasu sassan suka tara.

” Idan aka duba da kyau, har yanzu Arewa ce ke ciyar da kasar nan sannan kuma ay wanda ya fi kowa arziki a Nahiyar Afrika, wato Aliko Dangote dan yankin Arewa ne. Wani abu kuma da nake so kusa ni shine ‘yan Arewa ba su yin 419 kamar yadda ake kama ‘yan kudu suna yi sannan kuma wannan hanyar damfara da ake yi ta yanar gizo wato Yahoo-Yahoo duk ba ‘yan Arewa bane ake samu suna yin wannan munanan sana’a.

” Baya ga nan na yi kira ga matasan Arewa da sune suke fi yawa a yanki da su hada kai wajen ceto yankin daga jagulewa da lalacewa. Su fito su jagoranci yankin ba irin mu ba da munga jiya sannan muna ganin yau.

” Shekaru na 59, yanzu bai kamata ace wai ina gwamna ba. Amma kuma gashi haka ya kasance. ”

El- Rufai yayi wannan bayanai ne da kira ga matasan Arewa a taron wani kungiyar Matasan Arewa da aka yi a Kaduna ranar Asabar.

jaridar The Nation ne ta ruwaito cikakken bayanin abubuwan da suka gudana a wannan taro.

Share.

game da Author