Buhari ya sake nada Boss Mustapha da Abba Kyari a kan mukaman su

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha a kan aikin sa.

Sannan kuma ya sake nada Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari shi ma a kan na sa mukamin.

Wannan sake nadawar da aka yi musu makonni biyar bayan sake rantsar da Buhari a kan mulki karo na biyu, ta fito ne daga cikin wata sanarwa da Babban Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya sa wa hannu a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sake nadin Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma Shugaban Ma’ikatan Fadar Shugaban Kasa a kan mukaman su.”

“Wannan sake nadi da aka yi musu ya fara ne tun a ranar 29 Ga Mayu, 2019.”

An nada Kyari tun cikin 2015 bayan rantsar da Shugaba Buhari a kan mulki bayan nasarar zaben da ya yi a 2015.

An nada Boss Mustapha mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya, a cikin Oktoba, 2017, bayan tsige Babachir Lawan da aka yi, wanda aka kama da laifin yin harkallar kwangilar datse ciyawa a sansanonin masu gudun gudun hijira.

Wadannan nade-nade biyu, su ne Buhari ya fara yi tun bayan sake rantsar da shi a karo na biyu.

Share.

game da Author