Buhari ya jingine shirin gina wa Fulani Rugage

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shirin gina wa Fulani makiyaya rugage.

Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi ne ya bayyana haka a yau Laraba.

Ya yi bayanin ne bayan fitowa daga taron Majalisar Gudanarwa kan rikicin Fulani makiyaya da manoma.

An gudanar da taron a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

“Mu na sane da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Shirin Kafa Rugage, saboda shirin ya ci karo da Shirin Inganta Kiwon Dabbobi na Gwamnatin Tarayya. Shirin Kafa Rugage dai ya na karkashin Ma’aikatar Gona da Albarkatun Kasa ne.”

Kwamitin dai a karkashi jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo,ya tsara wasu shirye-shiryen hanyoyi mafita daga rikicin makiyaya da manoma.

Ruga dai tsari ne da gwamnatin tarayya ta shigo da shi, da nufin hada kai da jihohin da suka amince a kafa matsugunai ga Fulani makiyaya domin killace su wuri daya, yadda za a gina musu makarantu, asibitoci, wuraren ban-ruwar dabbobi, da sauran ababen more rayuwa.

An nemi yin haka ne domin kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa sanadiyyar rikicin Fulani makiyaya da manoma, satar shanu da kuma sauran hare-haren garkuwa da mutane da ake fama a Arewacin kasar nan.

Sai dai kuma duk da wasu jihohi 12 sun nuna goyon bayan su a yi shirin, sauran jihohin kasar nan sun yi kememe, sun nuna rashin amincewar su.

Jama’a da dama a Arewaci da kudancin kasar nan sun ki amincewa da shirin.

Yayin da a Arewa, jama’a na ganin kamata ya yi gwamnati ta fara maida hankali wajen gyara wa wadanda hare-hare ya lalata wa gidaje tukunna, a kudu kuwa ana ganin kamar kaka-gida ne ake neman a tilasta musu Fulani a kan su.

Duk da Fadar Shugaban Kasa ta fito ta bayyana alfanun shirin, hakan bai hana milyoyin mutane sun yi masa fassara ta daban ko ta siyasa ba.

Share.

game da Author