Shugaba Muhammadu Buhari ya cire Shugaban Hukumar Inshorar Lafiyar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (NHIS), Usman Yusuf.
Buhari ya tsige shi watanni 10 bayan dakatar da shi da aka yi, sakamakon wata dambarwar da ta faru tsakanin sa da hukumar gudanarwar NHIS da kuma tsohon ministan Harkokin lafiya, Adebowale.
Bayan dakatar da shi cikin 2018, an dora wa hukumar gdanarwar NHIS ta ci gaba da gudanar da al’amurran hukumar.
Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya, Bode Akinola ne ya fitar da sanarwar cewa Buhari ya cire Yusuf sakamakon bayanan da kwamitin bincike ya damka masa.
A madadin sa, a yanzu Buhari ya amince da nadin Mohammed Sambo a matsayin sabon Shugaban Hukumar NHIS.
Tun bayan dakatar da Usman Yusuf, an nada Sadiq Abubakar ne a matsayin shugaban riko.
RIKICIN NHIS
Hukumar NHIS ta shiga rikicin shugabanci da kuma zargin harkalla tun bayan da Yusuf ya zama shugaba.
Kafin a cire shi jiya Litinin, an dakatar da shi a karo biyu. Ya karbi shugabancin NHIS a cikin watan Yuli, 2016
Kafin dakatarwar farko, sai da Ministan Lafiya na lokacin Isaac Adewole ya dakatar da shi a cikin Yuli, 2017.
Sai dai kuma a cikin watan Fabrairu na 2018, Buhari ya maida Yusuf a kan aikin sa.
Watanni kadan kuma sai hukumar gudanarwar NHIS ta sake dakatar da shi.
Yusuf da Hukumar NHIS da Ministan Lafiya na lokacin, Adewole, sun rika zargin juna da aikata zambar kudade.
Sau da dama Yusuf na cewa shi nai aikata laifin komai ba, maimakon haka, shi ne ake so a ga bayan sa, domin masu wawurar kudade su rufe harkallar da suka yi, kuma saboda ya hana su ci gaba da yin harkallar.
Rikici sai da ya yi kamarin da har Majalisar ta gayyaci Ministan Kasafin Kudi, Udo Udoma, ta Harkokin Kudi, Kemi Adeosun, na Lafiya Isaac Adebowale da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da su bayyana su yi mata bayanin hakikanin gaskaiyar yadda aka cire naira bilyan 10 daga asusun ajiyar Hukumar Inshorar Kiwon Lafiya ta Kasa, NHIS.
BAN TABA CIN KO KWANDALA BA -Yusuf, kafin sake dakatar da shi
Wannan kwatagwangwama dai ta fito fili ne a a lokacin bayan da majalisar ta gayyaci Shugaban Hukumar wanda aka maida aiki kwanan a lokacin, bayan an dakatar da shi.
Farfesa Yusuf Usman ya yi bayanin cewa bai ga dalilin da za a dora masa alhakin salwantar naira bilyan 10 na NHIS ba, alhalin bai ci nanin ba, nanin na neman cin sa.
Daga nan sai Yusuf ya fara warware zare da abawa cewa:
“A da dai wannan naira bilyan 10 ta na cikin Asusun Bai-daya (TSA) na hukumar NHIS ajiye a Babban Bankin Tarayya CBN. Wata rana sai Ministar Kudi ta rubuto wasika, ta ce kamata yay i NHIS ta kasance wuri ne da zai rika samar wa gwamnatin tarayya kudin shiga.
“Ta rubuto min wasika, wadda a yanzu haka ina da kwafin cewa za a cire wadannan naira bilyan goma daga asusun NHIS, a bai wa gwamnatin tarayya.
“Kuma hakan ita Ma’aikatar Harkokin Kudin ta yi, ta cire kudaden tare da masaniyar Minstan Harkokin Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Ministan Kiwon Lafiya da kuma masaniyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya.”
Yusuf ya kuma shaida wa kwamitin majalisa cewa kamfanomin MHO sun rike makudan kudade ta yadda kawai shi ya zama kamar wani ‘jami’in karbo bashi kawai.’
Idan ba a manta ba, Ministan Lafiya ne ya dakatar da shugaban na NHIS, kuma ya kafa kwamitin bincike.
Kafin sannan, an yi ta kai ruwa rana inda Yusuf ya rika zargin ministan da yi barankyankyamar kudade.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya maida Yusuf kan aikin sa, a bisa dalilin cewa kwamitin da ya bincike shi na da wata kullalliya a kasa, kuma an kasa kama shi da wani tartibin laifi.
Sai dai kuma a yanzu an cire shi har an nada sabo, bayan ya shafe watanni goma a dakace.