Boko Haram sun kashe Kanar da wasu sojoji biyar

0

Sojoji shida cikin su har da wani Kanar sun rasa ran su a wani gumurzu da Boko Haram a jiya Laraba.

Baya ga Kanar din kuma an tabbatar da cewa akwai wani Kaftin a cikin wadanda Boko Haram din suka kashe.

Sannan kuma su ma sojojin sun kashe Boko Haram masu yawa.

An kai musu harin ne misalin kar 6:00 na yamma a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, a lokacin da sojojin ke kan sintiri a karkashin Sojojin Ko-ta-kwana na Birged na 29.

Har zuwa lokacin buga labarin dai Hukumar Tsaro ta Sojoji ba ta bayyana wannan lamari ba, sannan kuma kakakin yada labaran su, Sagir Musa bai dauki kiran wayar da PREMIUM TIMES ta yi masa kafin a buga wannan labari ba.

PREMIUM TIMES ta boye sunayen wadanda suka rasa rayukan na su, saboda ba mu tabbatar da ko an sanar da iyalan su ko ba a kai ga sanar musu ba.

Watanni da dama kenan sojoji na kauce wa bayyana sunayen wadanda aka kashe a wajen gumurzu da Boko Haram, cikin su kuwa har da wa Laftanar Kanar biyu wadanda kashe cikin watanni biyu da su ka gabata.

Wata majiya a cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kashe sojojin shida a jiya Laraba kusa da sansanin su a Jakana.

An kuma ce wadanda aka nema aka rasa daga cikin sojojin tuni sun koma sansanin su.

Sannan kuma an kara kai daukin wasu zaratan sojoji daga Hedikwatar Zaratan Ko-ta-kwana da ke Benisheikh.

Majiya ta ce tuni an kai gawarwakin sojoji shida da aka kashe a asibitin sojoji da ke Maiduguri.

Share.

game da Author