BIDIYO: Yadda Sanata ya mam-mari mace a kantin saida azzakarin roba

0

An kama Sanatan da ya fi sauran sanatoci mafi kankantar shekaru, ya na jibgar wata mata a cikin kantin da ake sayar da azzakarin roba da sauran kayan da mata ke jima’i da su na roba.

Lamarin ya faru ne a ranar 11 Ga Mayu, kafin a rantsar da su, a Abuja.

PREMIUM TIMES ta mallaki bidiyon yadda aka yi rikicin.

Sanata Elisha Abbo, wanda ya ke wakiltar Shiyyar Adamawa ta Arewa, ya hau matar da duka ne daga kawai ta je ta na ba shi hakurin kada ya doki mai tsaron kantin.

Sanata ya yi ikirarin cewa matar ta zage shi, shi ya sa ya hau ta da duka, kuma ta ce masa mashayin giya, bugagge wanda ya sha ya yi mankas.

Ya doki matar a gaban wani dan sandan mobal, wanda maimakon ya raba rigimar, sai ma ya yi kokarin kama matar.

An kai karar wannan fada a ofishin ‘Yan Sanda na Maitama, da ke kan titin Nile, amma sai suka ce sai an samo masu lambar sanatan kafin su iya yin wani abu tukunna.

TAMBELE DA BULKARAR ‘YAN GIYA

Wadda aka doka dai ba ki yin magana haka shi ma main kantin ya ki cewa komai, saboda su na tsoron kada sanatan ya yi musu bi-ta-da-kulli. Shi ma lauyan wadda aka doka din bai yi magana ba da PREMIUM TIMES ta tuntube shi.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta yi kokari inda ta samu wadansu da komai ya faru a gaban su, amma su ma suka ce a rufa musu asiri, kada a bayyana su, saboda tsoron abin da zai taba lafiyar su.

Sanata Abbo, wanda dan jam’iyyar PDP ne, ya shiga kantin wanda ake saida azzakarin roba tare da wasu kilakan sa guda uku.

Ya shiga ne tare da su a ranar wata Asabar, 11 Ga Mayu, 2019.

Sun je ne su sayi azzakarin roba da sauran robar da mata ke jima’i da ita. Haka PREMIUM TIMES ta tabbatar.

Jim kadan da shigar su, sai daya daga cikin matan da Sanata Abbo ya shiga kantin tare da su, ta fara kyara amai a cikin kantin.

Wannan ne ya sa mai kantin ya nemi matar da ke aman cewa ai kamata ya yi ta fita waje ta yi aman, ba wai ta tsaya cikin kantin ta na kyara amai ba, tunda ita ba karamar yarinya ba ce.

An ce hankalin Sanata Abbo ya tashi, ganin yadda daya daga cikin ‘yan matan sa ta rika kyara amai. Sai kawai ya zargi mai kanti cewa wai ya zuba guba ce a cikin A.C din kantin, har ta yi wa budurwar sa lahani.

Mai tsaron kanti ta ce to idan an zuba guba, me ya sa duk sauran wadanda ke ciki ba su kamu ba, sai yarinyar sa daya?

Wannan ya kara harzuka shi, har ta kai su ga cacar-baki a tsakanin su.

PREMIUM TIMES ta kalli bidiyon, kuma ta ga yadda Sanatan ya koma waje ya zauna a kan wani janareto, ya na kiran jami’an tsaro domin su kai masa dauki.

Sanata Abbo, dan shekara 41 da haihuwa, ya shaida wa dan sandan cewa ya kama mai kantin. Ita kuma mai tsaron kanti ta yi sauri ta kira mahaifin ta, kuma ta shaida masa cewa Sanata Abbo ya kira ‘yan sanda sun a shirin tafiya da ita.

Abbo ya cewa mai kanti ta daina kiran wani a waya, saboda ya na magana da ita. Amma ta ki dainawa. Ana iya ganin wani a cikin bidiyon da nufin fizge wayar ta.

Daga nan kuma sai wata kawar mai kantin ta zo ta na ba sanata hakuri.

A cikin fushi sai kawai Sanata Abbo ya harzuka, ya yi kan kawar mai kanti, ya rika daddalla mata mari, har a cikin idanu. Ya kira ce mata ‘mutuniyar banza.’

Daga nan sai ya nemi a kama mai kanti da kuma kawar ta. Kuma ya rika cewa ya ji haushin da ta kira shi dan giya. Daga nan ya rika yin barazanar cewa zai ji mata ciwo, kuma ya sa a rufe kantin na ta. Amma tunda shi tsohon kwastoman su ne, ba zai sa a rufe din ba.

WASHEGARIN SAFIYAR DA AKA YI MARKABU

PREMIUM TIMES ta gano cewa matar da aka daddalla wa mari, mai jego ce, ta na shayar da karamin yaro. An garzaya da ita asibiti, aka yi mata magani inda tsananin mari ya kumbura mata idanu da kuma sauran ciwukan da ya ji mata.

Sanata Abbo bai biya ta kudin magani ba, kuma bai nuna jinkai ko tasayin dukan da ya yi ma ta ba. Bai kuma roke ta afuwa ba.

Maimakon haka, sai ya koma kantin domin ya tabbatar cewa idan kyamara mai gani-har-hanji (CCTV) ba ta dauki bidiyon abin da ya faru kwana daya a kantin ba.

An shaida masa cewa ai kyaramar ba ta aiki, amma duk da haka sai da ya yi musu barazana cewa idan har bidiyon ya fita duniya aka gani, to za su yaba wa aya zakin ta.

Ganin haka sai wadda aka daddalla wa mari, tare da lauyan ta, ta kai kara ofishin ‘yan sandan Maitama, a ranar 14 Ga Mayu.

Jami’an tsaro sun ce ba su san inda za su samu Sanata Abbo ba.

Shi kuma lauyan ta, ya nemi sanatan ya ba ta hakuri, tare da biyan dukkan kudaden maganin da ta kashe.

Sannan kuma su na neman a binciki Sanata Abbo tare da gurfanar da shi a kotu.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Sanata Elisha Abbo kafin ta buga wannan labari, amma bai maida amsar sakon tes da aka yi masa ba, kuma bai amda kiran lambar sa da wakilin mu ya yi ba.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu maganar ba ta zo gaban teburin sa ba, amma zai so wadda aka ci wa zarafin ta same shi, domin ya san yadda zai kamo batun markabun sasai da sosai.

Share.

game da Author