BARNO: Kotu ta kori karar da aka kalubalanci zaben Gwamna Zulum

0

Kotun Koli ta kori karar da Idris Mamman-Gatumbwa ya kalubanci zaben fidda-gwanin da APC ta yi wa Gwama Babagana Zulum na Jihar Barno.

Mai Shari’a Jonn Okoro wanda ya karanta hukuncin a madadin sauran alkalai ne ya karanto korar karar.

“Kotun Koli ta kori wannan karar ce biyo bayan janyewar da lauyan mai kara ya yi a madadin mai kara, ba tare da wani ja-in-ja ba.

Dama kuma Kotun Daukaka Kara da ke Jos ce ta tafa yin fatali da karar da aka shigar wadda aka fara kalubalantar zaben da APC ta yi wa Zulum, tun a cikin watan Maris.

Daga nan sai Mamman-Gatumbwa shigar da kara a Kotun koli, ganin cewa bai gamsu da shari’u biyu da Babbar Kotun Tarayya a karkashin Mai Shari’a U Onyemenam ya yanke hukunci ba.

Sannan kuma bai yarda da Shari’ar Kotun Daukaka Kara ta Jos ba.

Kotu ta amince da hukuncin da kotunan baya suka zartas cewa karar da Mamman ya shigar ba ta da wata madogara.

Sannan kuma musamman an shigar da kara ce bayan wa’adin kwanaki 14 da aka amince cewa wanda bai amince da sakamakon zabe ba to ya garzaya kotu.

Zulum shi ne ya yi nasara a kan abokin karawar zaben gwamnan Barno na PDP.

Shi ya gaji Sanata Shettima wanda a yanzu sanata ne bayan ya kammala wa’adin shekaru takwas da ya yi ya na gwamna.

Shi ya maye gurbin Sanata Bukar Abba Ibrahim a Majalisar Dattawa.

Share.

game da Author