Bana shakka ko tsoron EFCC – Inji Saraki

0

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa bai aikata wani laifin da a yanzu Hukumar EFCC ke kokarin tuhumar sa da su ba.

Ya kuma kara da cewa shi bai shiga kafafen yada labarai ya na cacar-baki da EFCC ba.

A cikin watan Mayu ne dai EFCC ta shafa wa wasu gideje jan fenti, tare da ikirarin cewa ta tabbatar Saraki ne ya saye su a hannun Kwamitin Sayar da Kadarorin Gwamnatin Tarayya da Shugaban Kasa ya kafa.

EFCC ta ce Saraki ya sayi gidajen ne ta hannun kamfanin harkokin danyen mai fetur din nan wato Shell.

Cikin wani sabon zargi kuma, EFCC ta ce Saraki ya kwashi kudi daga asusun Gwamnatin Jihar Kwara har naira bilyan 12, tsakanin 2003 zuwa zuwa 2011 lokacin da ya yi gwamnan Jihar Kwara.

EFCC ta ce a banki aka cire kudaden gabadayan su.

EFCC ta ce an cire kudaden ne domin Saraki ya biya kudin bashin banki, wadanda ya yi amfani da naira bilyan 1.36 ya sayi gidaje masu lamba 15, 15A, 17, 17A a kan titin Macdonald da ke Ikoyi, Lagos. Dalili kenan ta kwace gidajen daga hannun sa.

Kakakin EFCC Tony Orilade ya ce babu wani kamfen a kafafen yada alabarai da Saraki zai rika yi a kan Magu, domin ya karkatar da shari’ar da EFCC ke kokarin gurfanar da shi.

Sai dai kuma kakakin Saraki, Yusuf Olaniyonu, ya ce EFCC din ce ma ke kamfen na bata sunan Saraki, ba Saraki ne ke yi a kan Magu kamar yadda EFCC ke ikirari ba.

Ya ce EFCC ta yi azarbabi domin bata wa Saraki suna, inda ta bayar da takardun bayanan tuhumar da ake yi wa Saraki ga wata jarida, ta buga domin kokarin bata Saraki.

Ya ce, “Mu na mamakin yadda jim kadan bayan shigar da kara da kwafen takardu a Babbar Kotun Tarayya kuma EFCC za ta raba takardun ga wata jarida domin a buga a kan Saraki. Amma kuma su ne wai za su ce Saraki na kamfen din bata wa Shugaban EFCC suna a jaridu.”

Daga nan sai ya ce Saraki ba ya tsoron komai, ba ya tsoron shari’a da kowa, saboda ya san bai aikata laifin komai ba.

Daga nan ya ce EFCC kame-kame kawai ta ke yi, kuma Saraki zai tsallake duk wani tarkon neman kama shi da laifi, kamar yadda ya yi nasara a Kotun Koli, bayan shari’ar da aka yi masa a Kotun CCT.

Daga nan sai ya gwasale EFCC cewa har wasu shari’u sun sake bincikowa wadanda sau biyu ana kai Saraki kotu kuma duk ya na yin nasara.

Sai ya yi karin haske cewa wannan bi-ta-da-kulli da ake yi masa a yanzu, cin zarafin ’yancin sa ne a matsayin sa na mai ‘yanci kamar kowa.

Ya ce Saraki ya shigar da kara, inda ya nemi kotu ta kare masa ‘yancin sa kamar yadda kowa ya ke da ‘yanci a kasar nan.

Share.

game da Author