Sanata Danjuma Goje mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, ya bayyana cewa ko da wasan kwaikwayo bai taba fuskantar tuhumar zargin wawurar naira bilyan 25 ba.
Haka Goje, tsohon gwamnan Jihar Gombe ya bayyana a cikin wani bayani da ya fitar a yau Alhamis.
Lauyan Sanata Goje mai suna Paul Erokoro ne ya fitar da sanarwar a madadin sa, ya na cewa ikirarin da ake yi wai an tuhumi Goje da salwantar da naira bilyan 25 a lokacin da ya ke gwamnan jihar Gombe, ba gaskiya ake yayatawa ba.
Erokoro ya ce bayanan da ake yadawa a kafafen yada labarai game da Goje, karkattaun bayanai ne.
Lauyan ya fitar da wannan bayani ne, biyo bayan rahotannin da aka rika watsawa masu bayyana yadda aka soke tuhumar da kotu ke wa Goje, wadda aka rika zargin cewa saboda ya janye wa Sanata Ahmad Lawan takarar shugabancin Majalisar Dattawa ne aka soke masa tuhumar ta zargin wawurar naira bilyan 25.
Ya ce naira bilyan 9 ne ake tuhumar Goje, ba naira bilyan 25 ba.
“Batun ana neman naira bilyan 25 a hannun Goje, duk jaridu ne suka kirkiri adadin kudaden.
“Gaskiyar abin da aka tuhumi Goje ana nema a hannun sa, su ne wajen naira bilyan 8 ba bilyan 25 ba.
“Daga cikin kudin kuma naira bilyan 5 bashi ne daga bankin Access Bank, wanda aka ciwo domin kammala wasu ayyukan raya kasa da suka hada da asibitoci, filin saukar jiragen sama na Gombe, ayyukan samar da ruwan sha, titina masu tarin yawa, Otal din Gombe Jewel, makarantu da ayyukan samar da hasken lantarki a yankunan karkara.
“Banki ya tabbatar wa kotu cewa duk an yi wadannan ayyukan, Su ma masu bincike daga EFCC sun gamsu da cewa an yi ayyukan, kuma sun bincika, sun kuma shaida wa kotu cewa duk an kammala ayyukan.”
Sauran kamar yadda lauyan ya fada, sun hada da bashin aikin harkokin noma na naira bilyan 1, shi ma Babban Bankin CBN ya gamsu da cewa an yi amfani da lamunin yadda ya kamata.
Akwai kuma gudanar da wani aikin abinci na Gidajen Saukar baki na naira bilyan daya, sai kuma samar da kayan karatu ga makarantun jihar na naira bilyan 1.6.
Ya ce dukkan tuhume-tuhume 19 da ake yi masa a kotu, duk an tabbatar da rashin sahihancin su.