Hukumar kwastam ta karyata labaran da ake ta yadawa wai wani jami’inta mai suna Nura Dahiru, ya nemi ya dare kujerar shugaban hukumar ranar Litini a Abuja.
Kakakin rundunar Joseph Attah ya sanar wa PREMIUM TIMES cewa Nura ya garzayo hedikwatar hukumar a safiyar Litinin yana sanye da kaye dauke da mukamin mataimakin shugaban hukumar Kwastam, Wato DCG.
Attah ya ce ko da suka tambaye shi ko me ya sa ya saka wadannan kaya da rataye da mukamin DCG sai ya fara sumbatu, ta inda yake hawa ba ta nan ya ke sauka ba. Daga nan ne suka gane cewa lallai wannan jami’i bashi da lafiya ne.
” Da muka gano haka sai muka garzaya da shi asibiti domin a duba shi.
A karshe Attah ya roki mutane da su taya jami’in da addu’a sannan ati watsi da karerayin da ame yadawa wai ya nemi ya dare kujerar shufaban hukumar ne, Hameed Ali.