Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira da babbar murya ga jam’iyyar su ta PDP cewa ta gaggauta ladabtar sa Sanata Elisha Abbo.
Ya yi wannan kiran ne bayan ya kalli bidiyon da PREMIUM TIMES ta buga inda sanatan ya ke dalla wa wata matar aure mari, a kantin saida azakarin roba, a Abuja.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne tsakanin 1999 zuwa 2007, yace ya kalli bidiyon, kuma ya san Abbo sosai da sosai, amma kuma wannan ba zai hana idan ya yi rashin gaskiya, ko ya aikata ba daidai ba, ya goyi bayan sa.
Daga nan sai ya shawarci Abbo da ya gaggauta neman afuwa wajen matar, tare da biyan dukkan kudaden maganin da ta kashe a asibiti, sakamakon kumbura mata fuska da ya i a lokacin da ya mam-mare ta.
Daga nan kuma ya yi kira ga uwar jam’iyyar su PDP da ta ladabtar da Sanata Abbo, domin ya bata wa jam’iyyar suna, kuma idan aka yi haka, zai zama darasi ga wani ko wasu a nan gab aba zai sake irin wannan bahallatsa da tambada ba.
Tuni dai wannan rikici ya game kasar nan, tare da bangarori da kungiyoyi da dama na kiran a hukunta Sanata Abbo.
Abbo shi ne Sanata mafi kankantar shekaru. Shekarun sa 41 da haihuwa.