Asusun tallafa wa jami’o’I (TETFund) za ta tallafa wa jami’ar koyar da kimiya da fasaha na ‘Abdu Gusau’ dake Talatan-Marafa a jihar Zamafara da Naira biliyan daya.
Kakakin gwamnatin jihar, Yusuf Idris ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da gwamna Bello Matawalle yayi da shugaban hukumar, Suleiman Bogoro a Abuja.
A ganawan da suka yi gwamna Matawalle ya bayyana wa Bogoro yadda yake kokarin ganin ya inganta fannin ilimi a jihar.
Matawalle ya yaba wa kokarin da hukumar ke yi a karkashin shugabancin Bagoro musamman a bangaren tallafa wa jami’o’in kasar nan inda ya ke bayyana cewa samun goyan bayan hukumar zai taimaka wajen farfado da manyan makarantun kasarnan.
Matawalle ya kara da cewa gwamnati za ta yi amfani da wannan tallafi domin samar da kayan aiki da gyara gine-ginen dake wannan kwaleji na ‘Abdu Gusau’.