Arewacin Najeriya yana da girman kasa da tarin al’umma. Wannan yanki shine yake da jihohi 19, kuma ya rayu cikin nasibi da taimakon Allah.
Duk da cewa mutanen Arewa suna da sauna da karancin karatun Boko bayan samun kasancewar Najeriya a matsayin kasa mai ‘yanci, hakan bai hana mu samun nasarar zama a shugabancin kasar ba.
A cikin rayuwar Najeriya, Arewa ce take da dogon zangon mulki, tun lokacin da Ingila ta qyanqyashi Najeriya a matsayin kasa. Sunayen shugabannin da suka mulki Najeriya daga yankin Arewa sune :-
– Sir Abubakar Tabawa Balewa (1959 – 1966 Served for 7years)
– Gen Yakubu Gowon (1966 – 1975, Served for 9years)
– Gen Murtala Ramat Muhammad (1975 – 1976, served for 1year)
– Alhaji Shehu Shagari (1979 – 1983, served for 4years)
– Gen Muhammadu Buhari (1983 – 1985, served for 2years)
– Gen Ibrahim Badamasi Babangida (1985 – 1993, served for 8years)
– Gen Sani Abacha (1993 – 1998, served for 5years)
– Gen Abdulsalami Abubakar 1998 – 1999, served for 1year)
– Umaru Musa Yar adua (2007 – 2009, served for 2years)
– Muhammadu Buhari (2015 – to date, still serving).
Duk wanda ya duba shugabannin da na bayyana zai fahimci cewa ‘yan kudu bai wuce shekara 16 suka yi ba a shugabancin Najeriya. A takaice, ga iya shugabannin da suka fito daga yankin kudu :-
– Nnamdi Arizikwe (1959 – 1966, served for 7years)
– Gen Arqui Ironsi (15th Jan 1966 – 29th Jul 1966, served for 44 days)
– Gen Olusegun Obasanjo (1976 – 1979, served for 3years)
– Chief Earnest Shonnikan (3 months interim government)
– Chief Olusegun Obasanjo (1999 – 2007, served for 8years)
– Dr Goodluck Ebele Jonathan (2009 – 2015, served for 6years)
Zan iya cewa duk irin nasibin da Arewa ta samu wajen shugabanci tsahon shekara 43 bai yi tasiri ga yankin ba saboda halin da mutanen cikinsa suke ciki bayan manyan Arewan na farko sun sadaukar da rayuwarsu wajen kare yankin.
Tun bayan rasuwar su Sardauna da Tafawa Balewa, muka samu rauni wajen jajircewa akan matsalar ‘yan uwanmu. Wasu daga cikin wadanda sun ci alfarmar su Sardauna amma su basu yadda aci tasu ba bayan rasuwar su Sardauna.
Mun samu kanmu a halin talauci, jahilci, rashin tsaro da manufa saboda mutanen yankin basa yin abun da ya dace wajen gina mutanensu da tsayawa wajen kare ra’ayin al’umma sosai a gwamnatin tarayya. Shiyasa duk binciken da za ayi akan talauci da jahilci, a Arewa yafi yawa.
Misali, a binciken da UNICEF tayi akan yara wanda basa zuwa makaranta (Out of school children OSC) arewa ce a gaba. A shekarun baya Shugaba Buhari yace mun fi kowa jahilci da talauci. A wata shekara mutum 7 ne kacal suka ci WAEC a Zamfara. Wannan dalilin ne yasa duk wani tsari da yazo daga gwamnatin tarayya muke kasancewa koma-baya a ciki saboda mutanenmu basu da gogewa da kishin mutanensu kamar abokan zamanmu.
Misali, tunda aka kafa shirin Npower bamu ta6a ji wani ya binciki yadda ake tafiyar da abun ba don ayi maganin hanyoyin da ake cire mutanenmu ko kin daukarsu. Saidai kawai wadanda muka ji suna neman a rushe shirin saboda ba a basu dama ba sun yi ha’inci. Yakamata manyan da suke da dama a gwamnati su tashi tsaye su taimakawa matasa a gwamnatance kamar yadda muke ganin abokan zamanmu ana yi musu. Yin hakan zai bawa matasanmu qaimin taimakawa na baya, tunda suma anyi musu.
Allah ya shiryar damu.