Bayan tashin hankaƙi da ya auku tsakanin ƴan shia da jami’an tsaro a Abuja ranar Litini, sufeto janar din ƴan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya garzaya fadan shugaban ƙasa domin ya yi masa bayanin abinda ya faru.
Jim kaɗan bayan tattaunawar su da shugaban Muhammadu Buhari, Sufeto Adamu ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa cewa ya ziyarce shugaba Buhari ne domin yayi masa bayanin abubuwan da suka faru.
” Nayi masa bayanin abubuwan da suka faru. Sannan na gaya masa cewa an samu dawowan zaman lafiya a garin Abuja yanzu.
Adamu ya ce shugaba Buhari ya gargaɗi jami’an tsaro da su tabbata sun tsare rayukan mutane da dukiyoyin su.
Bayan haka a yammacin litinin din ne PRNigeria ta ruwaito cewa an kashe wani babban jami’in ɗan sanda a arangaman jami’an tsaro da ‘Ƴan shi’a.
Jami’in da ya rasa ransa mai muƙamin mataimakin ƙwamishinan ƴan sanɗa ne.
Babbake motocin hukumar NEMA
A wannan zanga-zanga da ƴan shi’a suka yi yau a Abuja, mutane da dama sun rasa motocinsu bayan smasu zanga zanga sun ciccinna musu wuta.
Cikin motocin da aka babbakr har da motoci biyu na Hukumar NEMA dake ajiye a bakin titi.
Kakakin hukumar Sani Datti, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar tayi hasarar waɗannan motoci nata ne masu ɗan karan tsada a dalilin wannan gumurzu da jami’an tsaro suka ti da ƴan shi’a.
Idan ba a manta ba‘Yan shia sun fito zanga-zangar ci gaba da kira da suke yi ga gwamnati da ta saki shugaban su Ibrahim El-Zakzaky dake tsare tun a shekarar 2015.
Sun faro zanga-zangar ne daga mahadar Nitel inda suka dunguma zuwa Sakatariyar Abuja. A hanya suna Kabarbari suna cewa Allah ya kashe shugaban Amurka Trump, Allah ya kashe Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A daidai sun Iso Sakatariyar ne sojoji suka nemi tsaida su amma hakan bai yiwu ba daga nan sai aka fara batakashi a tsakanin su.
‘Yan shi’an sun rika jejjefa wa motoci bamabaman kwalba da akayi da fetur ciki har da motocin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa da wasu na mutane da dama.
Shugaban ‘yan shi’a Yahaya Mohammed da ya zanta da wakilin mu yace sun fito zanga-zangan su ne salin- alin kafin Sojoji suka far musu.
“Ba mu bane muka far wa sojoji, sune suka tsakale mu muna zanga-zangan lumanar mu.” Inji Yahaya.
Wannan ba shine bane karon farko da ake arangama da jami’an tsaro ‘yan shia a Abuja. Ko a kwanakin baya an kashe ‘yan shia biyu sannan an harbi ‘yan sanda biyu a Majalisar kasa a wani zanga-zangar su.
Discussion about this post