APC ta dakatar da Inuwa Abdulkadir daga Jam’iyyar

0

Jam’iyyar APC ta sanar da dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar yankin Arewa Maso Yamma Inuwa Abdulkadir.

Kakakin jam’iyar Lanre Issa-Onilu ne ya sanar da haka a takarda da ya rabawa manema labarai.

Jam’iyyar APC a mazabar Magajin Gari dake Sokoto wanda itace mazabar Inuwa, ta dakatar da shi tun a kwanakin baya. Sannan kuma reshen jam’iyyar na jihar Sokoto ta tabbatar da Korar a wancan lokaci.

” Jam’iyyar APC ta kasa ta nada kwamiti domin a warware matsalar dake tsakanin Inuwa da jam’iyyar a Sokoto domin cikin korafin da suka yi akan sa shine wai yayi wa Jam’iyyar PDP aiki ne a zaben gwamna amma hakan bai yiwu ba.”

Lanre yace Inuwa bai iya kare kansa a gaban kwamitin ba wadda a dalilin haka uwar jam’iyyar ta rattaba hannu a tabbatar da dakatar dashi.

Share.

game da Author