Wasu likitoci dake kasar Faransa sun gargadi mutane da su rage shan zaki da yawa domin dage wa ci yana kawo cutar daji.
Jagoran binciken Eloi Chazelas ya bayyana cewa sun gano haka ne daga sakamakon binciken da suka gudanar a jikin wasu beraye.
“Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa kayan zaki na dauke da sinadarin dake hadassa cutar daji baya ga ciwon siga,hawan jini,cututtukan dake kama zuciya da kiba dxa yake sawa.
A dalilin haka suke kira ga mutane da su nisanta kan su daga shan kayan zaki musamman lemun kwalba.
Idan ya kama a iya nika ‘ya’yan itatuwa domin a sha cewa sun fi lemon kwalba da ake sha.
Kwanakin baya Kamfanin sarrafa Lemu na Coca Cola ya gargadi mutane da su rage shan zaki don lafiyar su.
Manajan kula da cinikayya na kamfanin Gbolahan Sanni, ne ya sanar da haka a wajen kaddamar da sabbin lemu da ga kamfanin.
Ya ce sabbin Lemun da suka fitar lemu ne da ya kunshi kayan itatuwa da jiki ke bukata.
Ya kuma yi kira ga mutane da su dinga amfani da irin wadannan lemu domin lafiyar jikin su sannan su rage shan zaki da yawa.
Bayan haka wasu masu bincike a kasar Amurka sun bayyana yawan haka na haddasa cutar hanta.
Shi dai wannan bincike anyi shi wa musamman mutane masu bakin fata dake kasar Amurka.
Sakamakon binciken ya nuna cewa cutar hanta na kama tsofaffin da suke yawaita shan zake a lokacin da suke da kurucciya.
A dalilin haka wadannan masu binciken suke kira ga matasa da su rage yawan shan zaki domin guje wa kamuwa da cutar hanta a musamman lokacin da suka tsufa.