Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa an yi garkuwa da darektan kotun daukaka kara na kotun shari’a dake Kaduna.
Sabo ya sanar da haka ne ranan Alhamis da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kaduna.
Ya ce DPO din dake Sabon Tasha ne ya sanar da shi abin da ya faru.
“ Ya ce wasu masu garkuwa da mutane sun far wa gidan Hussain Manjalo dake zama a Doka Mai Jama’a kauyen Kujama a karamar hukumar Chikun da karfe 6:30 na yamman Laraba inda suka sace Hussain da uwargidan sa Aishatu Muhammad sannan suka kashe dansa Abdulrrauf Muhammad.”
Sabo yace ” Yan sandan dake aikin fatattakar masu garkuwa da mutane sun hada hannu kungiyoyin ‘yan bangan dake wannan yanki domin ceto wadanda aka yi garkuwa da.
Garkuwa da mutane yayi matukar kazancewa musamman a wadannan yankuna. Idan ba a manta ba a lokuttan baya ne masu garkuwa irin haka suka arce da wanin faston cocin ECWA da mabiya 14 a Dankande dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.
Tun a wancan lokaci, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Yakubu ya bayyana cewa dakarun ‘yan sandan sun fantsama domin ceto wadannan da aka yi garkuwa da.