An sasanta tsakanin mutumin da ya sha dukan tsiya da Shugaban Karamar Hukuma

0

Idan ba a manta ba a wani bidiyo da ya kareda shafunan facebook a yanar gizo ya nuna yadda wasu maza guda biyu ke lakada wa wani mutum dukan tsiya da ‘belt’ hisa zargin wai ya zagi shugaban karamar hukuma.

A na magana a bidiyon da harshen Annang sannan a ciki za a ga yadda wani ke dukan Abraham sannan wani na taka kan Abraham da kafa.

Mai duka idan ya tsula masa bulala sai yace masa “Za ka kara?!

Shikuwa Abraham cikin rudewa da radadin zafi sai yace yace “A’a ba zan kara ba.”

Bisa ga wadannan tambayoyi da wadannan maza ke wa Abraham akwai alamun cewa Abraham ya yi wa William aiki ne wanda shi William ya ki biyan sa.

A dalilin haka sai Abraham ya hau shafin Facebook ya yi rubutun da game da kin biyan sa da ba ayi ba.

“Nawa ne kudin da kake bin chairman?

“Duk aikin da nayi masa Naira 75,000 ya kamata ya biya ni.

“Da bai biya ka ba sai ka hau hau facebook ka na zagin sa ko?!

“Za ka goge rubutun da ka yi?!

“Zan goge!

Bayan haka da ya faru, Abraham ya garzaya kotu domin neman abi masa hakkin sa. Bayan alkali ya saurari karar sai kuma shi Abraham ya janye wannan karar a wani zaman kotun yana mai cewa lallai ya yarda su sasanta a waje.

An dai biya Abraham kudin sa naira 70,000 sannan an kara masa naira 50,000 da ya rasa a wajen aikin. Baya ga haka an saya masa sabuwar wayan hannu da ya fashe a lokacin da ake dukan sa.

Share.

game da Author