Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa an samu raguwa a adadin yawan mutanen dake fama da ciwon ido da ke kira ‘Trachoma’.
Gwanaye sun bayyana cewa kwayoyin cutar ‘Chlamydia’ ne ke haddasa ciwon inda rashin magance cutar da wuri ke kawo makanta.
“A kan kamu da cutar Chlamydia ne ta hanyar jima’I ko kuma ta yin amfani da ban dakin da bashi da tsafta.
Alamun ciwon idon sun hada kaikayin ido, hawaye, kwantsa, jan-ido da sauran su. Sannan shan hannu, yawan kusantan masu dauke da cutar da yin amfani da kayan sawarsu kamar tsuman goge fuska ko na share jiki na daga hanyoyin da za a iya kamuwa da cutar.
A dalilin haka malaman asibiti suke kira ga mutane cewa da zaran an kamu da cutar sanyi na ‘Chlamydia’ kamata ya yi a gaggauta zuwa asibiti domin samun magani.
Malaman asibiti sun ce yin fida a ido da shan maganin ‘Antibiotics’ na cikin hanyoyin dake hana ciwon makantar da mutum sannan yin amfani da ruwa mai tsafta wajen wanke ido, tsaftace muhalli, nisanta kai daga masu dauke da cutar na cikin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
ABIN DA BINCIKE YA NUNA
Sakamakon binciken da WHO ta yi ya nuna cewa akalla mutane miliyan biyu a duniya sun makance a dalilin kamuwa da wannan cuta. Sannan kashi 60 bisa 100 daga cikin su yara kanana ne ‘yan kasa da shekara biyar.
A 2002 mutane biliyan 1.5 ne suka kamu da cutar sannan a 2019 mutane miliyan 142 ne ke dauke da cutar a duniya.
Sakamakon ya kuma nuna cewa adadin yawan mutanen dake bukatan fida a ido a dalilin wannan ciwo ya ragu inda a 2002 mutane miliyan 7.6 ne ke bukatan fida sannan a 2019 miliyan 2.5.
A yanzu haka kasashen duniya 44 ne ke fama da cutar sannan WHO da sauran kungiyoyin bada tallafi kokarin ganin an kawo kaeshen wannan cuta ta hanyar dakile yaduwar sa.